Zaɓen 2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jama’a Kan Kalaman Ƙiyayya Da Labaran Ƙarya A Kano
[ad_1]
Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya gargaɗi duk wanda ke yaɗa kalaman ƙiyayya ko labaran ƙarya a jihar cewa zai fuskanci hukunci mai tsauri, yayin da ake ƙara ɗaukar matakai don tabbatar da zaman lafiya gabanin zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne a Taron Matasa kan Zaman Lafiya na Kano karo na biyu (Kano Youth Peace Summit 2.0), wanda rundunar ’yansanda ta shirya tare da haɗin guiwar YOSPIS da Gidauniyar Aminu Magashi Garba.
- An Yi Taron Dandalin Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Beijing
- Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ɗaukar Likitoci ‘Yan Asalin Jihar Aiki Kai-tsaye
CP Bakori ya ce labaran ƙarya da kalaman ƙiyayya a kafafen sada zumunta da na gargajiya na barazana ga zaman lafiyar jihar kuma na iya janyo tashin hankali.
“Ba za mu bari kowa ya tayar da hankalin jiharmu ba. Duk wanda aka samu da laifin yaɗa kalaman ƙiyayya ko labaran ƙarya zai fuskanci hukunci,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga ’yan jarida, matasa da shugabannin al’umma da su riƙa yaɗa haɗin kai a kafafen sada zumunta.
Shugaban Gidauniyar Aminu Magashi Garba, Aminu Magashi, ya ce taron ya zo a kan lokaci, kasancewar lokutan zaɓe kan kasance cike da tashin hankali da labaran ƙarya.
Ya ce su da abokan hulɗarsu za su shirya horo da wayar da kai domin yaƙar labaran ƙarya da ƙarfafa rahoto na gaskiya.
Sauran masu jawabi, ciki har da Mai Ba Gwamna Shawara kan Tsaron Al’umma, Ambasada Maimuna Umar, da Daraktar YOSPIS, Zainab Nasir Ahmed, sun yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, al’umma da matasa.
[ad_2]
Source link