’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, Sun Ƙone Gidaje A Ƙauyukan Kwara

[ad_1]

’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Woro da Nuku da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara da yammacin Talata.

Maharan sun kashe mutane tare da ƙone gidaje da dama, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargici.

  • Sin Ta Yi Kira Ga Dukkan Kasashen Da Ke Son Zaman Lafiya Su Dakile Burin Japan Na Sake Shan Damarar Soji
  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ɗaukar Likitoci ‘Yan Asalin Jihar Aiki Kai-tsaye

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen Woro da misalin ƙarfe 5 na yamma.

Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar daga yankin, Hon. Aliyu Mande, ya tabbatar da harin, inda ya ce ana zargin mutum 10 sun rasa rayukansu.

Ya ƙara da cewa an sanar da hukumomin tsaro da shugabannin ƙaramar hukuma game da lamarin.

Babban Mataimaki na Musamman kan Tsaro ga Gwamnan Jihar Kwara, Alhaji Muhideen Aliyu, shi ma ya tabbatar da harin.

Sai dai ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, domin rahotanni na ci gaba da shigowa daga wuraren da abin ya faru.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin mummunan aiki.

Ya ce jami’an tsaro na ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga daga ƙauyukan.

Gwamnan ya jajanta wa al’ummar Woro da Nuku, musamman iyalan da suka rasa ’yan uwansu da dukiyoyinsu.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *