Tasirin Wayar Hannu Wajen Bunkasar Soyayya
[ad_1]
Daga Rabiat Sidi Bala
Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi soyayya, inda wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu “Ko ya wannan batun yake na cewar; Duk namijin da zai wuni daya ko kwana daya bai kira mace ba, baya sonta kawai burge shi take yi. Shin mene ne gaskiyar maganar?, ko akwai wasu alamomi da suke nuni da cewa, namiji yana son mace ko da hakan ya faru ba wai burge shi kawai take yi ba?, Wadanne abubuwa ne ya kamata mata su kula da shi sosai, musamman idan namiji yana son su ko da sun samu sabani?”
Ga dai bayannan nasu kamar haka:
Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos a Jihar Filato:
Abin da ya kamata a fahimta shi ne akwai bambanci tsakanin yadda namiji yake jin shaukin soyayya a zuciyarsa da yadda mace take ji. Halittar namiji da mace game da soyayya ba iri daya ba ce. Sannan a mazan ma halayensu da wayewarsu game da abin da ya shafi soyayya ba daya ba ne. Ba lallai ne sai namiji na yawan kiranki a waya shi ne yana sonki ko ya damu da ke ba. Kowa da yadda yake bai wa abubuwan rayuwarsa muhimmanci. Wani mace ko wacce yake shaukin so ita ce farkon abin da yake yawan tunawa. Wani kuma duk son da yake miki, sai ya samu natsuwa da wurin da ya kamata, sannan zai yi magana da wacce yake so, a wajensa wannan ita ce kulawa. Ba a auna zurfin son da namiji ke yi wa mace da yawan kiran waya. Yadda namiji ke mutunta ki, da yi miki magana cikin girmamawa, da tattalin buƙatunki, da ɗaukaka ki a wajen ýan’uwansa da abokansa, duk alamu ne na soyayya da fifitawa. Akwai yanayin da namiji yana son mace, amma saboda sanin cewa ba zai iya aurenta ba, ko ba shi da damar aurenta a lokacin, zai riƙa rage yawan yadda yake kiranta da ba ta kulawa, don kada shaƙuwar su ta yi yawa, ya zama an samu damuwa a lokacin rabuwa. A duk lokacin da mace ta fuskanci haka daga wanda take so to, ta yi ƙoƙarin jawo hankalinsa yadda za su fahimci juna, don ta gane matsayin soyayyarsu da kuma uzurorin sa.
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
A lokuta da dama samari na kasancewa masu zakuwa da matan da suke so tare da kauna, wanda hakan tana faruwa ne daga wajen wasu, a inda wasu kuma ba ta haka suke nuna soyayyarsu ba. Alamomin su ne; ba da kulawa, neman masoyiya a duk inda take, bata taimako ta hanyar da ya dace, neman yafiya tare da bata uzuri, ziyartarta domin ganin halin da take ciki, sauraren kukanta tare da share mata, bata lokaci domin samun fahimtar juna, kiranta a waya domin jin muryar juna, gaisuwa tare da fatan alkhairi, tura mata sakonin soyayya tare da fatan alkhairi a lokutan da zai yi wuya ta iya mantawa da irin faruwar hakan, dauke mata kewa a lokacin da take cikin damuwa, daga karshe kasancewa abokin wasanta domin nuna mata kauna.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya wannan batu ba haka yake ba, domin soyayya daban, yawan kiran waya daban. Ita kulawa tana da nau’i kala-kala ba wai kiran waya kadai ba. Eh hakika alamomin suna da yawa, domin yin auren ma kadai yana nuna alamar akwai soyayya kuma zamantakewa ta yau da gobe dole ne ake yi wa juna uzuri. To abubuwan suna da yawa domin kowanne mutum da irin abin da yake burge shi a zamantakewar aure, kuma mutuntawa da kiyaye dokokin shari’a yana matukar kara kauna a tsakanin ma’aurata.
Sunana Fatima Nura Kila Jihar Jigawa:
Eh, za a iya cewa haka maganar take, domin duk ‘busy’ din namiji ai dole ya samu ‘free time’ ko da a wanni 2 ne, ko sau 1 ya kira ai ana tare. Rashin kira gaskiya wannnan alama ce ta ba a tare da ke. Alamomin su ne, duk inda yake, koda bai yi kira ba zai yi ‘tedt’ kan cewar wasu uzururruka sun sha masa kai.
Sunana Ibrahim Garba Bizi, Damaturu, Jihar Yobe:
Gaskiyar magana ba lallai ba ne. Namiji na iya samun dalilai kamar; aiki, damuwa, ko tsoro da ya sa bai nemi mace kowace rana ba, amma har yanzu yana sonta. Amma idan ya yi sakaci akai-akai, hakan na iya nuna rashin kulawa ko damuwa da ita. Alamomin namiji yana son mace: Ya rika nuna kulawa da damuwa a lokuta daban-daban, yana kokarin zama kusa da ita da magana da ita. Abubuwan da mata za su kula da su ne; Fahimtar halin da namiji yake ciki, ba yanke hukunci da wuri ba, kula da soyayya mai tsarki ba tare da takura ko zargi marar tushe ba.
Sunana Shamsiyya Sabo, Jihar Kebbi:
Gaskiya ne wannan batun, domin muddin namiji yana sonka da gaske to, wallahi ba zai iya wuni guda ba tare da ya ji muryarka ba, idan ma an samu to, bai fi ace jifa-jifa ba, irin kafin a sami hakan za a dade wannan kuma ai ka yi wa mutum uzuri. Amma mutumin da za a ce aikinsa kenan ai kai ma ka san dole ba ta taka yake ba, yana da wasu a gefe.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano daga Jihar Kano:
Ba gaskiya ba ne, Akwai su kam. Kadan daga ciki sune; yawan zancenta, yawan tuno da halinta na kirki da kuma yawan bibiyar ‘yan’uwanta. Su rika yin abin da yake so ko da bai ce ba, su rika nuna masa soyayyar iyayensa da ‘yan’uwansa, su rika kiyaye duk wani abin da zai sa ransa ya baci. Allah ya sa mu dace, Amin.
Sunana Hafsat Sa’eed:
Eh, gaskiya yana faruwa. Namiji kam idan har yana sonka to, ba zai iya kwana daya bai ji muryarka ko bai kira ka ba, sai dai kam idan ba so ne na tsakani da Allah ba, ba kuma soyayyarka bane a cikin zuciyar sa ba. Alamomin da suke nuna ana sonka shi ne; mutum zai rika kula da kai, minti kadan yana jin yaya ka ke ko kuma da ya ji shuru zai tabo ya ji ya lafiyar ka take. Amma mutum yayi buris sai dai kai ka neme shi to, alamomi ne da suke nuna cewa baya son ka, burgewar ma dai gashi nan ne dai.
Sunana Aliyu Idris (Sarkin Yakin Malumma), daga Jihar Jigawa:
Gaskiya ne, idan har namiji yana kaunar budurwar sa, to babu shakka duk bayan lokuta zai rika yawan tunata a kan lokaci. Domin kara inganta soyayyar su, musamman idan tana nuna masa kauna ta gaskiya. Saboda haka, so yana da matukar tasiri wajen bayyana shi ga zuciyar da take kyautata masa akodayaushe. Duk lokaci da ki ka fahimci cewa namiji baya baki kulawa ta musamman a kan lokaci, kamar: rashin baki lokacin yin soyayya, rashin kiranki a waya kamar sau biyu zuwa uku a duk rana, Ko kuma yawan tura sakonni dake dauke da kalaman soyayya da sauransu. To duk wadannan wasu matakai ne da za su tabbatar nagartar soyayyarsa a tsakanin ku.
[ad_2]
Source link