SUBEB ta dauki nakasassu 23 aikin koyarwa a Jigawa

[ad_1]



Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta ɗauki ma’aikata 23 masu nakasa da suka cancanta domin koyarwa a makarantun firamare na jihar.

Shugaban SUBEB, Farfesa Haruna, ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da ilimi mai haɗa kowa da kowa tare da ba da dama iri ɗaya ga dukkan ’yan ƙasa.

Farfesa Haruna, ce an yi haka ne bayan korafe-korafen da masu nakasa suka yi, wadanda suka shiga jarabawar daukar malamai a baya amma ba su samu shiga cikin jerin wadanda aka dauka ba.

Ya bayyana haka ne a tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin dandalin Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE).

Waɗanda abin ya shafa, waɗanda sunayensu aka gabatar tun da farko ta Hadaddiyar Kungiyar Nakasssu ta Kasa (JONAPWD) reshen Jigawa, sun riga sun amsa kiran hukumar bisa umarnin hukuma.

Shugaban JONAPWD na jihar Jigawa, Adamu Sha’aibu, ya yaba wa Farfesa Haruna, yana bayyana matakin a matsayin babban ci gaba da ke nuna adalci, kulawa da kuma shugabanci mai haɗa kowa.

Ya ce wannan amincewa ta dawo da bege da kwarin gwiwa ga al’ummar masu nakasa, tare da jaddada cewa matakin ya yi daidai da ƙa’idodin duniya na haɗa kowa da kowa da kuma kare haƙƙin masu nakasa.

Kungiyar JONAPWD ta kuma yi kira da a duba sauran masu nakasa da suka cancanta amma ba su samu shiga cikin tsarin ba tukuna, tare da jaddada aniyarta na ci gaba da yin aiki tare da hukumomin gwamnati domin tabbatar da cikakkiyar haɗa kowa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *