AFCON 2025: Zan Taimaka Wa Uganda Ta Doke Super Eagles Duk Da Mahaifina Ɗan Nijeriya Ne – Ikpeazu
[ad_1]
Kafin wasan ƙarshe na rukunin C da Nijeriya za ta buga da ƙasar Uganda da yammacin yau Talata na gasar AFCON 2025 da ke gudana a Morocco, ɗan wasan gaban Uganda wanda haifaffen Nijeriya ne, Uche Ikpeazu ya ce ya mayar da hankali kan taimaka wa ƙasar domin su doke Super Eagles duk da cewa asalinsa ɗan Nijeriya ne.
“A bayyane yake ina cikin farin ciki, burinmu na samun cancantar ci gaba da buga gasar na nan a cikin zukatanmu don haka ina farin ciki da hakan,” in ji shi.
- Kotu Ta Tisa Ƙeyar Malami Zuwa Gidan Yarin Kuje
- Kuri’un Jin Ra’ayin Al’ummun Kasa Da Kasa Sun Kara Jaddada Amincewa Da Kasar Sin
“Amma a bayyane yake muna son samun nasara a wasan, don haka idan zan iya cin ƙwallo kuma mu samu nasara a wasan, da hakan ne abin da na fi so duk da kasancewata ɗan Nijeriya”.
Ɗan wasan gaban ya amince da alaƙar da ke tsakaninsa da Nijeriya ta hanyar mahaifinsa amma ya bayyana inda ya mayar da hankalina, “ni rabin ɗan Nijeriya ne, daga nan ne mahaifina ya fito don haka ba shakka za a samu jinin Nijeriya a cikin jinina, amma kuma na mayar da hankalina kacokan wajen ganin Uganda ta samu nasara a kan Nijeriya” in ji Ikpeazu.
Dangane da yiwuwar zura ƙwallo a raga a wasan da za su buga da Nijeriya, Ikpeazu ya ce, “A wasan ƙwallon ƙafa, wani lokacin son zuciyarka tana rinjayarka, don haka, ban sani ba amma idan na zura ƙwallo, hakan zai yi kyau, duk da dai mafi muhimmanci shi ne mu samu maki uku.”
Idan ba a manta ba LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa Nijeriya ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin zagayen ‘yan 16 bayan ta haɗa maki shida daga wasanni biyu da suka gabata na rukunin.
[ad_2]
Source link