Trump Zaman Lafiya Yake Samar Wa Nijeriya Ba Yaƙi Ba – Riley Moore
[ad_1]
Ɗan majalisar Amurka, Riley Moore, ya ƙaryata zargin cewa Shugaba Donald Trump na ƙoƙarin haddasa yaƙi a Nijeriya.
Moore ya yi wannan bayani ne a shafinsa na X a ranar Litinin, bayan wani hari da Amurka ta ƙaddamar a sansanin ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya a ranar Kirsimeti, wanda aka ce an aiwatar da shi bisa umarnin Trump.
- Sin Za Ta Kyautata Tsarin Lura Da Kudin Kasar Na Dijital A Shekara Mai Kamawa
- ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Nemi A Dakatar Da Aiwatar Da Dokokin Haraji
Ya ce, “Shugaba Trump ba ƙoƙarin ƙaddamar sa yaƙi yake yi a Nijeriya ba. Yana kawo zaman lafiya da tsaro ga Nijeriya da dubban Kiristoci da ke fuskantar tashin hankali da kashe-kashe.
“Harin da aka kai wa ISIS, wanda aka yi tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Nijeriya, ya bai wa Kiristoci a Nijeriya ƙwarin guiwa.”
Leadership Hausa ta ruwaito cewa Moore ya bayyana a baya cewa Trump na mayar da hankali wajen dakatar da kashe-kashen Kiristoci a Nijeriya.
A baya-bayan nan Moore ya jagoranci wata tawagar Amurka domin binciken zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya, inda ya ziyarci Jihar Benue don ganawa da shugabannin addini, sarakuna, da kuma mutane da suka rasa muhallinsu.
[ad_2]
Source link