An binne Sarkin Zuru, Muhammad Sani Sami
[ad_1]
An yi jana’izar marigayi Sarkin Zuru, Manjo Janar (mai ritaya) Muhammad Sani Sami Gomo II, a gidansa da ke garin Zuru a Jihar Kebbi.
Ya rasu a wani asibiti a Landan a ranar Asabar da ta gabata, bayan fama rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.
An yi jana’izarsa bayan idar da sallar Juma’a.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Zuru, Alhaji Suleiman Muhammad Tanko, ne ya jagoranci sallar jana’izar.
Manyan baƙi ne suka halarci jana’izar ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Sarkin Yauri.
Sarkin Gummi, Sarkin Anka, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris da luma Tsohon Ministan Tsaron Cikin Gida, Laftanal Janar (mai ritaya) Abdulrahman Dambazau na daga cikin waɗanda suka halarta.
Sauran da suka halarta sun haɗa da Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, Sarkin Kagara, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Sa’idu Dakingari, da Ministan Harkokin Jin-ƙai, Dokta Yusuf Tanko Sununu, da sauransu.
Shettima, ya isa Zuru da safiyar ranar Juma’a, inda ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi ga Jihar Kebbi, Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.
A madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar, mutanen Kebbi da masarautar Zuru.
Ya kuma yaba wa marigayin bisa sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da rokon Allah Ya bai wa iyalansa da al’umma haƙurin rashinsa.
An girmama marigayin, ta hanyar ufe dukkanin kasuwannin Zuru.
Tituna da hanyoyin da za su kai mutum zuwa masallacin da aka yi jana’izar suka cika maƙil da jama’a.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link