ADC Ta Yi Fatali Da Sabon Jadawalin Zaɓe Da INEC Ta Fitar

[ad_1]

Jam’iyyar ADC ta yi fatali da sabon jadawalin zaɓe da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar, tana iƙirarin cewa an tsara shi ne don ware jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanya hannu, jam’iyyar ta ce jadawalin da aka sake tsarawa ba kawai shirin gudanarwa ba ne, wani tuggun siyasa ne da rai raunana ƴan adawa.

ADC ta yi iƙirarin cewa sabbin abubuwan da aka ƙaƙaba a cikin dokar zaɓe ta 2026 sun yi wa jam’iyyun adawa sauri yawa.

A cewar sabon jadawalin zaɓeni, za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu tsakanin 23 ga Afrilu da 30 ga Mayu, 2026. Duk da haka, jam’iyyu dole ne su miƙa cikakken rajistar mambobinsu ta na’urar zamani ga INEC kafin ranar 2 ga Afrilu, 2026, makonni kaɗan masu zuwa.

Jam’iyyar ta nuna cewa sashe na 77 na dokar, wanda ke cewa kowace jam’iyya da ta kasa gabatar da rajistar mambobinta akan lokaci, ba za ta gabatar da ɗan takara a wannan zaɓe ba. ADC ta bayyana wannan lamarin a matsayin wanda ya saɓa wa doka wacce aka saɓa.

“Wannan ba dokokin cikin gida ba ne. An ƙirƙiresu ne da gangan don sanya shinge ga ‘yan adawa daga shiga zaɓen da ke tafe,” in ji sanarwar.

ADC ta bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta riga ta fara tattara irin wannan rajista tun daga watan Fabrairu 2025, kafin ta samar da dokar, wanda ya ba ta babbar dama.

Ta ƙara da cewa yayin da jam’iyyar mai mulki ta kwashe kusan shekara guda tana yin shiri, ana sa ran sauran jam’iyyun adawa su kammala wannan tsari a kusan wata guda. ADC ta bayyana wannan a matsayin abin da ba zai yiwu ba a aikace.

Jam’iyyar ta kuma zargi cewa tasirin sabon jadawalin da dokar zaɓe sun bayyana Ƙarara cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ake share wa hanya don ya yi tazarce a zaɓen 2027.

Ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da ɗaukacin ‘yan Nijeriya daga ɓangarorin siyasa daban-daban su duba wannan jadawalin tare da haɗa kai da su wajen neman adalci. Ta yi gargaɗin cewa dimokuraɗiyya ba za ta iya wanzuwa ba idan an shamfiɗa dokoki don fifita wani ɓangare guda ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *