Sojoji Sun Daƙile Harin Fashi Da Makami A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

[ad_1]

Sojojin rundunar sojin Nijeriya, babbar runduna ta 1 da ke aiki mai taken ‘Operation FANSAN YAMMA’ sun yi nasarar dakile wani harin fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, lokacin da sojoji da ke sintiri a hanyar suka sami kiran gaggawa game da harin fashi da makami a daidai kauyen Nasarawan Doka.

Sanarwa da Laftanar Kanar Shuaib Umar, Mukaddashin Darakta na Hulda da Jama’a na babbar rundunar soji ta 1, ‘ Operation FANSAN YAMMA’, ya sanya wa hannu, ta ce bayan samun kiran gaggawa, sojojin sun juya zuwa wurin kai tsaye inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan fashin, sannan suka kawar da barazanar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *