Babu gwamnan da ke juya akalar jam’iyyar APC — Yilwatda

[ad_1]



Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce babu wani gwamna da ke juya akalar jam’iyyar.

Ya bayyana cewa dukkanin shawarwarin da ake zartarwa a APC ana yin su ne a matakin ƙasa, ba ta hannun gwamnonin jihohi ko shugabannin jihohi ba.

Ya bayyana hakan ne cikin shirin ‘Sunset a Jay FM’, Jos, Jihar Filato.

ya ce: “A faɗin ƙasar nan, babu wanda zai iya ɗaukar wani sashe na jam’iyya. Duk abin da za a yi a matakin jiha, ana tsara shi ne a matakin ƙasa.

“Wannan tsarin APC ne. Muna aiki bisa tsarin jam’iyya, ba bisa jin daɗi ko ra’ayin ƙashin kai ba. Babu shugaban ƙaramar hukuma, Gwamna, Sanata, ko wani mutum da ke da iko a APC, har da ni kaina.”

Ya ƙara da cewa APC ba ta da kwamitin amintattu saboda guje wa rikice-rikice.

Ya ce jam’iyyar mallakin jama’a ce, kuma jama’a su ne masu kula da ita.

Ya ce hakan ba tsarinsu ba ne, kamar yadda wasu jam’iyyu da wasu tsirarun mutane sarrafa su ba, tsarin APC ba shi da wani da ke sanya ido kan shugaban jam’iyya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *