Ƴan PDP Sun Fara Taruwa A Abuja Don Halartar Babban Taron Jam’iyyar Na Ƙasa
[ad_1]
Ƴan majalisar wakilan jam’iyyar PDP daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun fara isa Velodrome na filin wasa na ƙasa a Abuja. Ana sa ran sama da wakilai 2,500 za su halarci taron.
Taron na wannan ɓangare na PDP da Ministan Abuja, Nyesom Wike ke marawa baya, na da nufin zaɓen sabbin shugabannin jam’iyya. Hakan na zuwa ne bayan kammala zaɓukan cikin gida a jihohi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Bayar Da Lamba Ga Sabbin Daliban Firamare
- Kotu A Norway Ta Ɗaure Ɗan Wasan Nijeriya Kan Zargin Aikata Fyaɗe
Kwamitin riƙo na PDP ƙarƙashin Abdulrahman Mohammed da Sanata Samuel Anyanwu ne ke jagorantar shirye-shiryen taron. Sun jaddada cewa za a gudanar da taron kamar yadda aka tsara.
Sai dai wani ɓangare na PDP ƙarƙashin Tanimu Turaki ya nuna adawa da taron. Wannan ɓangare na samun goyon bayan gwamnoni Bala Mohammed da Seyi Makinde.
Ɓangaren gwamnoni ya garzaya Kotun Ƙoli na yana ƙalubalantar hukuncin da ya soke taron Ibadan na bara. Duk da haka, ɓangaren Wike ya dage cewa taron Abuja zai gudana kamar yadda aka tsara.
[ad_2]
Source link