Sojoji Sun Tarwatsa Gungun Masu Tayar Da Bam A Adamawa

[ad_1]

Rundunar Sojojin Nijeriya na atisayen haɗin kai (OPHK) ta tarwatsa wata ƙungiyar masu shirya harin bam na ƙunar baƙin wake tare da daƙile hanyoyin jigilar kayayyakin ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a Jihar Adamawa. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a Maiduguri ranar Litinin.

Sanarwar ta ce dakarun OPHK sun samu gagarumar nasarar ne yayin ci gaba da aiyukan kewaye da bincike da ake yi domin gano masu hannu a harin bam da aka kai Masallacin Kasuwar Gamboru a jajibirin Kirsimeti a Maiduguri. Biyo bayan sa ido na tsanaki kan wasu wurare, Sojojin sun kai sumame a unguwar Ƴan Lemo da ke Ƙaramar Hukumar Mubi ta Kudu a safiyar 5 ga Janairu, 2026.

  • Bayan Taka Nakiya, Sojoji 9 Sun Rasu, Wasu Sun Raunata A Borno
  • Gwamnatin Adamawa Ta Sanya Dokar Hana Fita Daga Lamurde Na Sa’o’i 24

A yayin sumamen, an kama mutane takwas da ake zargi, ciki har da manyan mutane biyu da ake zaton su ne ke jagorantar hanyar samar da kayan harin bam. Binciken da aka yi a gidajensu ya haifar da gano kuɗi, da wayoyin hannu, da takardun shaida, da katinan ATM, da kayan ado da sauran kayayyaki, waɗanda ake ci gaba da tantancewa domin tallafa wa binciken da ake yi. Wani wanda ke tsare a baya ya tabbatar da cewa manyan waɗanda aka kama su ne suka samar da kayayyakin haɗa bam ɗin IED.

A wani ɓangare na aikin, rundunar ta OPHK ta kama wani kayan man fetur da ake zargin an tanade shi ne domin ƴan ta’adda a garin Mayo Nguli da ke ƙaramar Hukumar Maiha a ranar 4 ga Janairu, 2026. Sojojin sun kwace jarkoki 45 na man fetur mai lita kimanin 1,125, bayan da masu safarar suka tsere suka bar kayan. Rundunar ta jaddada ƙudirinta na murƙushe hanyoyin ƴan ta’adda, tare da kira ga jama’a da su kasance masu sa ido da haɗin kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da ɗorewar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *