Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ya Sauka Beijing Domin Ziyarar Aiki
[ad_1]
Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sauka birnin Beijing a yau Laraba, domin ziyarar aiki da zai yi a kasar har zuwa ranar Jumma’a mai zuwa.
Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta hudu da Macron ya kawo kasar Sin, kuma ziyara ce ta mayar da alheri game da ziyarar da shugaba Xi ya kai kasar Faransa a bara mai dimbin tarihi, a lokacin da aka cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa.
A yayin ziyarar ta wannan mako, Xi zai tattauna da Macron domin yin hadin gwiwa wajen jagorantar bunkasa dangantakar Sin da Faransa a cikin sabon yanayi. Shugabannin biyu za su kuma yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan manyan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link