’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a wurin bikin aure a Kaduna

[ad_1]



Akalla mutum 13 sun mutu, yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama bayan ’yan bindiga a wurin wani bikin daurin aure a kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagoro ta Jihar Kaduna da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi.

Wani mazaunin kauyen mai suna, Shehu Bala, ya ce, ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 ne suka kutsa dakin taron bikin inda suka bude wa mutane wuta, mutum 13 suka mutu nan take.

A cewarsa, an garzaya da mutanen da suka samu raunukan harbi zuwa Babban Asibitin Kagarko, wasu mutum biyu da suke cikin mawuyacin halin kuma an wuce da su Kaduna domin ba su kulawa.

Shehu, wanda ya ce ba a kai ga tantance adadin mutanen da aka sace ba, ya bayyana cewa, “Abokaina biyu da ke cikin dakin taron a lokacin sun samu raunukan harbi. Amma babu wanda zai iya fadan ainihin yawan mutanen da aka yi garkuwa da su saboda karfin harbe-harben da ’yan bindigar suka yi.”

Wani shugaban al’umma a yankin ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa an yi jana’iza wadanda aka kashe, amma har zuwa lokacin ’yan bindigar ba su kira ba.

Ya ce maharan sun kai kusan awa guda sun a cin karensu babu babbaka, inda suka fasa shaguna suka kwashe kayan masarufi da magunguna a wani kemis.

Wata majiya a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Kagarko ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce ba a tabbatar da yawan mutanen da ’yan bindigar suka sace ba.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, ya ma tabbatar da faruwar lamarin, amma ya bayyana cewa cewa rundunar ba ta tantance yawan wadanda aka sace ba.

Ya ce, daga baya za ta fitar da  cikakken bayani, kuma jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Wakilinmu ya gano cewa Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe tare da Sanata Sani Musa (313) sun ziyarci Babban Asibitin Kagarko domin duka wadanda harin ya rutsa da su.

Wasu al’ummomi da dama, ciki har da Janjala, sun dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga, inda aka sace mutane 14, ciki har da wani dan banga da matarsa, kimanin makonni uku da suka gabata.

Har yanzu suna hannun masu garkuwa da su da ke neman Naira miliyan 14 a matsayin kudin fansa kafin su sake su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *