Majalisa ta kara yawan kuɗin yaƙin neman zaɓen ’yan takarar shugabancin kasa zuwa N10bn

[ad_1]



Majalisar Wakilai ta amince da ƙara yawan kuɗin yaƙin neman zaɓe da ’yan takarar shugaban ƙasa za su kashe daga Naira biliyan biyar zuwa biliyan 10.

Majalisar ta kuma ƙara yawan kudin da ’yan takarar gwamna za su kashe daga Naira biliyan 1 zuwa Naira biliyan 3.

An kuma ƙara yawan kuɗin da aka iyakance wa ’yan takarar Majlisar Dattawa da Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 500 yayin da ’yan takarar Majalisar Wakilai suke da damar kashe abin da bai haura Naira miliyan 250 ba, saɓanin Naira miliyan 70 a baya.

Ga masu son tsayawa takara don shiga Majalisar Dokoki ta Jiha kuwa, an ba su damar kashe abin da bai haura Naira miliyan 100 ba saɓanin Naira miliyan 30 a baya.

’Yan takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar daga Naira miliyan 30 zuwa miliyan 60, Kansiloli kuma daga miliyan 5 zuwa miliyan 10.

Sannan Majalisar ta amince cewa kada gudunmawar da wani mutum ko wani kamfani zai iya bai wa ɗan takara ta haura Naira miliyan 500.

Bugu da ƙari, Majalisar ta amince da wajabta wa Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) aike wa da sakamako ta hanyar amfani da intanet.

Majalisar ta Wakilai ta amince da waɗannan sauye-sauye ne bayan ta yi nazarin rahoton Kwamitinta a kan Al’amuran Zaɓe a wani ɓangare na garambawul ɗin da ake yi ga Kundin Dokar Zaɓe.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *