Mutuwar Imam Abdullahi Babbar Rashi Ne Ga Kiristoci – Yuhana Buru
[ad_1]
Babban Fasto Dakta Yuhana Buru ya bayyana rasuwar babban malamin addinin Musulunci a garin Barikin Ladi da ke Jihar Filato, Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin babba rashi ga Kiristoci, wanda ya voye mabiya addinin Kirista a gidansa a lokacin wani tashi – tashina a shekarar 2018.
Ya ce rasuwarsa ba na al’ummar Musulmi ne kawai ba, har da mabiya addinin Kirista da suke a jihohin arewa da kuma Nijeriya baki ɗaya.
- Imam Abdullahi Abubakar, Wanda Ya Boye Kiristoci 300 A Rikicin Filato Na 2018, Ya Rasu
- Imam Abdullahi Abubakar, Wanda Ya Boye Kiristoci 300 A Rikicin Filato Na 2018, Ya Rasu
Dakta Yuhana ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gana da wakilinmu kan rasuwar Sheikh Abdullahi Abubakar a wannan makon.
Dakta Buru ya ƙara da cewa a lokacin wannan matsalolin da suka faru a garin Barikin Ladi, marigayin ba tare da vata lokaci ba ya buɗe ƙofar gidansa, mabiya addinin Kirista suka shiga, wannan mataki da marigayin ya ɗauka a wancan lokaci shi ya zama silar ceton rayuka na mabiya addinin Kirista.
Sai fasto Yuhana ya ce wannan matakin son zaman lafiya da girmama abokan zama da Marigayi Imam Abdullahi Abubakar ya aiwatar, shi ya dace a yau mabiya addinin Kirista da mabiya addinin Musulunci su ɗauka, domin kawo ƙarshen matsalolin zaman doya da manja da ake yi a yau a wasu sassan Nijeriya.
A madadin mabiya addinin Kirista da suke arewacin Nijeriya da kuma Nijeriya baki ɗaya, Fasto Yuhana ya miƙa ta’aziyyar rashin marigayin ga iyalansa da gwamnatin Jihar Filato da ƙungiyoyin addinin Musulunci da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Dakta Sa’ad Abubakar III da Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam a Nijeriya da kuma sauran al’ummar Musulmi baki ɗaya.
[ad_2]
Source link