Budurwa Ta Tsere Da Motar Saurayinta Bayan Sun Kwana A Otel A Abuja

[ad_1]

Wata budurwa ta tsere da motar saurayinta bayan sun kwana tare a wani otel da ke unguwar Asokoro a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya shiga otel ɗin tare da budurwar ne da yammacin ranar Larabar da ta gabata.

  • Tsaro: Sojoji Sun Kwato Dabbobi 529 Daga Hannun ‘Yan Ta’adda A Katsina
  • Bayanan Ƙarya: Za A Iya Dakatar Da Ɗalibi Zana Jarabawar UTME Na Tsawon Shekara 3

Da misalin ƙarfe 7:12 na safe washegari, yayin da mutumin ke barci, budurwar ta shirya a hankali, ta ɗauki makullin motarsa, sannan ta fita zuwa wajen ajiye motoci.

An ce ta fita da motar ne bayan ta nuna kamar za ta je sayo wani abu a waje.

Bayan mutumin ya farka, sai ya gano cewa matar da motarsa duk sun ɓace.

Nan take ya kai rahoto ga jami’an tsaro.

Majiyoyi sun ce a cikin motar akwai muhimman takardu, kwamfuta da kuma kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba.

Kakakin rundunar ’yansandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce rundunar ’yansandan ta fara bincike tare da ƙoƙarin cafke matar da ake zargi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *