Matashi ya rasa ransa a kan soyayya a Yobe

[ad_1]



Wani matashi mai shekaru 20, Jibrin Saidu Lamido, ya rasa ransa bayan wani rikici a kan soyayya da ya auku  ƙauyen Gurdadi da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je zance wajen budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri.

Wata majiya ta ce wani mutum da ba a san ko waye ba ya zo wajensu, tare da tafiya da budurwar sannan ya ƙalubalanci Jibrin da ya biyo su idan shi “namijin gaske ne.”

Daga nan ne rikici ya ɓarke tsakaninsu, inda wanda ake zargi ya daɓa wa Jibrin adda a wuya.

“An garzaya da shi zuwa asibitin Kumaganam amma likita ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji majiyar ’yan sanda.

Rundunar ’yan sandan jihar ta miƙa gawar mamacin ga iyayensa don yi masa jana’iza.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa suna ci gaba da neman wanda ake zargi, wanda ya tsere bayan aikata laifin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *