Doguwa Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano

[ad_1]

Umar Haruna Doguwa ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano bayan an cimma matsaya da aka yi a taron jam’iyyar da aka gudanar a daren ranar Talata.

Doguwa ya taɓa riƙe wannan muƙami kimanin shekaru 10 da suka gabata.

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 15
  • Kafar CGTN Ta Fitar Da Rahoto Game Da Hasashen Ababen Mayar Da Hankali Yayin Manyan Taruka Biyu Na Sin

An tabbatar da shi ne a taron da aka yi a filin wasa Sani Abacha, inda wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar suka halarta.

Shugaban kwamitin gudanar da taron, Rabiu Suleiman Bichi, ya ce an cike dukkanin muƙamai ta hanyar yin sulhu.

Ya bayyana cewa wakilai kusan 2,400 ne suka halarci taron, kuma duk sun amince da shugabannin da aka zaɓa ba tare da wata adawa ba.

Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Salisu Maje Ahmed Gwangwazo a matsayin Mataimakin Shugaba, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo Bichi a matsayin Sakatare, da Farfesa Nura Yaro Dawakin Tofa a matsayin Mataimakin Sakatare.

Haka kuma an zaɓi wasu domin riƙe sauran muƙamai domin tafiyar da harkokin gudanarwa.

An rantsar da sabbin shugabannin tare da kira a gare su da su bi kundin tsarin mulkin jam’iyyar tare da yin aiki cikin haɗin kai.

A jawabinsa na karɓar muƙamin, Doguwa ya gode wa shugabanni da wakilai bisa amincewar da suka nuna masa.

Ya yi alƙawarin tafiyar da shugabanci domin ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyya gabanin zaɓuka masu zuwa.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya sabbin shugabannin murna, yana mai cewa zaman lafiya da aka samu a taron alama ce ta ci gaban siyasa.

Ya buƙace su da su tabbatar da adalci, haɗin kai da dimokuraɗiyya a cikin harkokin jam’iyya.

Manyan ’yan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, Tijjani Abdullahi Gwarzo, Abdussalam Abdulkarim Zaura da Murtala Sule Garo, da sauransu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *