Ba zan tsaya takarar shugaban ƙasa ba a 2027 — Saraki

[ad_1]



Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa ko wata kujera ba a babban zaɓe na shekarar 2027.

Saraki ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

“Ba zan tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba,” in ji Saraki lokacin da aka tambaye shi ko zai yi takarar.

Sai dai ya jaddada cewa jam’iyyarsa ta PDP na nan daram duk da rikice-rikicen cikin gida da ake fama da su.

Ya ce iƙirarin da ake yi na cewa PDP ta mutu ko ta rushe ya samo asali ne daga saɓanin da ke tsakanin manyan ’yan jam’iyya, ba wai halin da jam’iyyar ke ciki a matakin ƙasa da tushe ba.

“Idan kana Abuja, za ka iya ganin haka saboda hayaniyar shugabanni, amma idan ka je jihohi da ƙananan matakai, za ka ga PDP na da ƙarfi sosai,” in ji shi.

Saraki ya kawo misalin Jihar Kwara, inda ya ce bayanan da yake samu daga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar na nuna cewa PDP na da karɓuwa a tsakanin al’umma.

Game da harkokin cikin gida kuwa, ya ce tun da farko ya yi adawa da taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, amma daga baya ya amince wakilan Jihar Kwara su halarta bayan an ba shi tabbacin cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC za ta sanya ido domin tabbatar da sahihancin taron.

Sai dai ya ce hukumar ba ta halarta ba, wanda a cewarsa ya kamata hakan ya sa a dakatar da taron.

Har ila yau, Saraki ya musanta jita-jitar cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, yana mai jaddada cewa yana nan a PDP.

Ya kuma soki jam’iyya mai mulki bisa gazawa wajen tabbatar da cikakkiyar dimokuraɗiyyar sauran jam’iyyun adawa.

Sai dai Saraki ya bayyana cewa ba shi da wata ƙiyayya ta ƙashin kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da ƙalubalen siyasar da ya fuskanta a lokacin da yake Shugaban Majalisar Dattawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *