2027: NNPP Za Ta Yi Nasara A Kano Ko Babu Gwamna Abba — Jigon NNPP

[ad_1]

Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya ce jam’iyyar za ta lashe zaɓen gwamnan Jihar Kano a 2027 ko da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da zama a jam’iyyar ko kuma ya koma APC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan jita-jitar cewa gwamnan na shirin ficewa daga NNPP bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu.

  • AFCON 2025: Dalilin Da Ya Sa Super Eagles Ba Ta Jira Bikin Karɓar Kyautar Tagulla Ba – NFF
  • Mataimakin Ministan Wajen Sin: Nuna Karfin Tuwo Ba Abun Da Zai Haifar Sai Koma Baya

Johnson ya faɗi hakan ne a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

A cewarsa, NNPP ta yi ƙarfi a Kano ko da ba ta riƙe madafun iko ba.

Ya ce jam’iyyar ta yi rawar gani a 2019, sannan kuma ta ci zaɓe a 2023 duk da cewa ba ta da gwamna, ’yan majalisa ko shugabannin ƙananan hukumomi a lokacin.

Johnson ya ce jam’iyyar ba ta damu da raɗe-raɗin sauya sheƙar ba, kuma tana da tabbacin za ta sake cin zaɓe a Kano a 2027, ko da Gwamna Abba yana tare da su ko kuma ba ya tare da su.

Jita-jitar ta ƙara ƙarfi ne bayan Gwamna Yusuf ya ziyarci Shugaba Tinubu a ranar Litinin.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya ce ziyarar ba ta da alaƙa da siyasa, illa tattaunawa kan matsalar tsaro, ciki har da kisan wata mata da ’ya’yanta.

Gwamna Abba ya lashe zaɓen gwamnan Kano na 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, inda ya doke ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

A ’yan watannin nan, raɗe-raɗin sauya sheƙarsa zuwa APC ta yi ƙarfi tare da rahotannin rashin jituwa tsakaninsa da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *