Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye

[ad_1]



Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kamaru da ake ci gaba da kirgawa ya nuna jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu gagarumin rinjaye a yankunan da a bayan Shugaba Paul Biya ya saba rinjaye.

Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 yana fuskantar abokan hamayya 11 cikin har da tsofaffin mukarrabansa, da ma tsoffin ministocinsa da ke neman kujerarsa da ya shafe shekara 43 a kai kuma yake namen wa’adi na takswas.

Cikinsu har da tsohon Ministan Yawon Bude Ido, Bello Bouba Maigari, da tsohon ministan Ayyuka, Bakary, wanda ya yi murabus a watan Yuli domin shiga takara kuma ya sama mafi shahara bayan doka ta haramta wa madugun adawa Maurice Kamto shiga zaben..

Biya ya ki yin tsokaci game da nasarar a lokacin da ya jefa kuri’arsa a birnin Yaounde ranar Lahadi, amma sakamakon farko sun nuna jam’iyyar FSNC wadda Bakary ya tsaya takara ta samu galaba a yankin da a bayan jam’iyyar CPDM ta Shugaba Biya ke da rinjaye.

Wani dan jarida da ke aikin sa ido kan zaben shaida wa wakilimu cewa jam’iyyar FSNC ta samu rinjaye a yawancin runfunan zaben da ke larduna bakwai na birnin Yaounde.

Kowacce daga cikin lardunan na da rumfunan zabe 40 zuwa 50, lamarin da ya mayar da Yaounde fage mai matukar muhimmanci a zaben kasar.

Bakary, wanda dan asalin yankin Garoua ne a yankni Arewa mai Nisa ya kuma doke Bello Maigari a yankin da su biyun suka fito.

Amma duk da haka Jam’iyyar CPDM tana bukatar samun gagarumar goyon bayan a yankin Ambazoniya – Arewa mai nisa da kuma yankin Kudu maso Yamma da kuma Arewa maso Yamma masu amfani da turancin Ingilishi.

Wani dan jarida ya bayyana cewa Bakary ya samu rinjaye a kuri’un da aka jefa a kasashen waje, in banda kasar Rasha.

“Karon farko ke nan tun shekarar 1992 da jam’iyyar adawa ta samu irin wannan rinjaye tun da wuri,” in ji shi.

Wadannan alkaluman wucin gadi ne a yayin da ake jihar Hukuamr Shari’a ta kasar za ta sanar da sakamakon zaben a hukumance cikin makonni biyu da ke tafe.

Ya ci gaba da cewa “Hukumar tana iya sauya sakamakon kuma Kotun Koli tana iya nada duk wanda ta ga ya dace da kujerar.”

Tsarin zaben Kamaru na zagaye daya ne, inda duk wanda ya fi samun kuri’u shi ne ke da nasara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *