An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja




Mazauna sun lakaɗa wa wata mata duka sannan suka ƙone ta ƙurmus kan zargin yi wa fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) ɓatanci a yankin Kasuwan-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wata muhawara ta taso a cikin shagon matar inda take abincin sayarwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, wani daga cikin kwastomomin matar ne cikin raha ya ce yana so ya aure ta domin ta zamo matarsa kamar yadda sunnar Ma’aiki (SAW) da tanadar, amma daga bisani lamarin ya haifar da cece-kuce har aka yi zargin ta furta kalaman ɓatanci.

Wani da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce an fara kai matar fadar Hakimin Kasuwan-Garba, inda daga nan aka miƙa ta hannun jami’an tsaro domin bincike.

Sai dai wasu gungun fusatattun matasa suka kwace matar mai suna Amaye daga hannun jami’an tsaron suka riƙa jifa da dukan da ya yi ajalinta.

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa yanzu haka ƙura ta lafa kuma harkokin yau da kullum sun kankama.

Kazalika, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa “da misalin ƙarfe 2 na ranar 30 ga watan Agusta, an samu rahoto cewa wata mata mai suna Amaye ta yi wasu kalamai da aka ɗauka a matsayin ɓatanci ga Annabi (SAW).

“Wannan lamari ya jawo fushin jama’a da suka kai mata farmaki suka ƙone ta kafin isowar ƙarin jami’an tsaro.

“Yanzu haka ana ƙoƙarin cafke waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin gudanar da bincike da gurfanar da su a kotu.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *