Tinubu ya naɗa Yuguda a matsayin mataimakin Gwamnan CBN

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Lamido Abubakar Yuguda, a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce naɗin zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da shi.

Onanuga, ya ce an yi naɗin ne bisa tanadin Sashe na 8(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya ta shekarar 2007.

An naɗa Yuguda ne, bayan tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Bala Bello, ya samu sabon muƙami a matsayin Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziƙi da siyasa.

Shugaba Tinubu, ya buƙaci su gudanar da ayyukansu da jajircewa, ƙwarewa da kuma sadaukarwa domin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Kafin wannan naɗi, Yuguda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Darakta Janar na Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari (SEC) daga shekarar 2020 zuwa 2024.

Yuguda ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya kammala digiri a fannin Accountancy a shekarar 1983.

Daga bisani a shekarar 1991 ya samu digiri na biyu a fannin Kuɗi, Banki da Harkokin Kuɗi a Jami’ar Birmingham da ke Birtaniya.

Shi mamba ne na Cibiyar Ƙwararrun Masu Lissafi ta Najeriya (ICAN) kuma yana da takardar shaidar Chartered Financial Analyst (CFA).

Ya fara aikinsa a shekarar 1984 a Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin babban mai kula da ayyuka a sashen harkokin kuɗaɗen waje.

Tsakanin shekarar 1997 zuwa 2001, ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziƙi a sashen Afirka na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) kafin ya koma aiki a CBN.

Daga bisani ya yi ritaya daga CBN a shekarar 2016 bayan ya yi shekaru shida yana riƙe da muƙamin Daraktan Sashen Kula da Ajiyar Kuɗi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *