Akwai Yakinin Cewa Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Za Ta Zama Muhimmiyar Kafa Ta Ingantaccen Bude Kofar Sin
[ad_1]
Kwanan nan, kasar Sin ta kaddamar da tsarin ayyukan kwastam na musamman a duk fadin tsibirin da ke karkashin tashar teku ta ciniki mai ‘yanci ta Hainan (FTP). Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Talata 23 ga wata cewa, yana da yakinin cewa, tashar FTP ta Hainan za ta zama wata muhimmiyar kafa ta ingantaccen bude kofar kasar Sin ga kasashen waje. Kasar Sin za ta kara bude kofa mai fadi, kuma za ta samar da karin damarmaki na ci gaba. Kuma wannan zai haifar da sabon kuzarin ci gaba ga samun wadata ta bai-daya a duniya.
Lin Jian ya ce, yayin da ake fuskantar karuwar rashin tabbas a tattalin arzikin duniya, matakin da kasar Sin ta dauka shi ne gabatar da kudurinta na bude kofa ta hanyar daukar matakai a aikace, domin yaki da kariyar cinikayya cikin azama, da sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin duniya mai bude kofa.
Ya kara da cewa, jerin abubuwan da kasar Sin ta hana ba da damar zuba jari daga waje sun ragu, sannan an sassauta takunkumin da aka sanya na shiga harkokin masana’antu, kuma an soke biyan haraji da kashi dari bisa dari ga dukkan kasashe masu karancin ci gaba da ke da huldar diflomasiyya da kasar Sin, kana an inganta manufar shigowa kasar ba tare da biza ba da kuma yada zango a kasar ba tare da biza ba.
Kazalika, Lin Jian ya kuma bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamba, kasar Sin ta kafa sabbin kamfanoni sama da 60,000 masu jarin kasashen waje, inda adadinsu ya karu da kashi 16.9 bisa dari a mizanin shekara-shekara, kuma adadin cinikin kayayyaki ya zarce RMB yuan triliyan 41, wanda ya karu da kashi 3.6 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Haka nan, ya ce kasar Sin ta ci gaba da kara zurfi da fadada bude kofarta, don zama maganadisu mai karfin gaske ga kasuwannin ketare, da kuma nuna juriya da kuzari a fagen cinikayya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link