GGI Da Kasar Sin Ta Gabatar Ta Samar Da Mafita Ga Kasashen Da Ke Cikin Mawuyacin Hali
“Babu mutane da yawa a can. An ce wurin mallakar Denmark ne, amma Denmark ba ta zuba masa ko sisi ba, kuma ba ta samar masa kariyar soja ba. An ce, a shekaru 300 da suka wuce, mutanen Denmark sun je wurin da jiragen ruwa, sai dai ina ganin a lokacin mu ma mun shiga jirgi mun je wurin.” Da muka zo karshen shekarar 2025, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake fara daukar mataki a kan tsibirin Greenland da ya nuna sha’awarsa tun farkon bana, inda ya nada gwamnan jihar Louisiana, Jeff Landry, a matsayin manzon kasar Amurka game da harkokin Greenland, kafin daga bisani ya yi kalaman na sama da ke ban dariya, kasancewar kowa ya san zuwa badi ne Amurka za ta cika shekaru 250 da kafuwa. Duk da haka, a wajen mai nuna fin karfi, ko tarihi ma ake iya sake rubutawa.
Alal hakika, matsalar Greenland ta shaida mawuyacin halin da kasa da kasa ke ciki ta fannin tsarin kulawa da harkokin duniya. In mun waiwayi shekarar 2025 da ke dab da karewa, za mu tarar da cewa: Rasha da Ukraine na ci gaba da gwabza fada da juna, wanda da wuya a ga karshensa, kuma rikicin da ya auku tsakanin Palasdinu da Isra’ila ya haifar da hasarorin rayuka sama da dubu 70, tare da raba mutane kusa miliyan biyu da muhallansu, duk da haka, Amurka ta yi ta jefa kuri’ar kin amincewa da daftarin tsagaita bude wuta da kwamitin sulhun MDD ya gabatar, har wa yau, shugaba Trump ya dauki matakin haraji na yi-min-na-rama kan kasashen duniya, wanda ya yi matukar lalata tsarin ciniki na tsakanin bangarori da dama… Lallai ana kara fuskantar matsalolin da suka shafi tsarin da muke da su wajen kulawa da harkokin duniya.
Sai dai abin farin ciki shi ne, a fuskantar matsalolin da ke gabansu, kasashe masu tasowa na kara hada kawunansu tare da daukar kwararan matakai, har ma suka zamanto wani muhimmin rukuni na inganta tsarin kulawa da harkokin duniya.
A wannan shekara, duniya ta shaida muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa wajen inganta tsarin kulawa da harkokin duniya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin kulawa da harkokin duniya, wato GGI a takaice, wanda hakan ya samar da gudummawar kasar wajen kara tabbatar da adalci ga tsarin kulawa da harkokin duniya, tare da karfafa matsayin MDD wajen jagorantar harkokin duniya. Kamar yadda Bahaushe kan ce, “faduwa ta zo daidai da zama”, shawarar ta samu goyon baya daga kasashe da kungiyoyin duniya sama da 150. Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Nijeriya, Charles Onunaiju ya ce, shawarar GGI ta kara wakilcin kasashe masu tasowa tare da kara fitowa da muryarsu, wanda hakan abu ne da Nijeriya da sauran kasashen Afirka suka dade suna nema.
A wannan shekara kuma, kasashen Brazil da Afirka ta Kudu sun karbi bakuncin shirya taron kolin BRICS da na G20, kasar Brazil a nata bangaren ta kuma shirya taron MDD kan sauyin yanayi. Abin lura shi ne, kasashe mahalarta taron MDD kan sauyin yanayi sun cimma daidaito ba tare da halartar kasar Amurka ba, matakin da masanan kasa da kasa suke kallonsa a matsayin sanarwar kasashe masu tasowa na dukufa a kan kafa tsarin kulawa da harkokin duniya mai karin adalci.
A wannan shekara, kasashen Afirka sun ci gaba da kokarin kare adalcinsu, inda suka ci gaba da korar sojojin kasashen yamma, har Faransa ta mika wasu sansanonin soja biyu ga Senegal, matakin da ya kawo karshen girke sojojin da kasar ta yi a kasashen yammacin Afirka da na tsakiyar nahiyar. Har wa yau, kungiyar tarayyar Afirka ta kira taron koli da ke da taken “kiyaye adalci ga ’yan Afirka da zuriyoyinsu ta hanyar biyan diyya”, wanda ya isar da sakon kasashen Afirka na tsayawa a kan kafafuwansu da ma gyara kura-kuran da aka tafka musu a tarihi. Sai kuma a Nijeriya, gwamnatin kasar ta ki yarda da bukatar kasar Amurka game da karbar bakin haure da ta kora daga kasar, duk da matsin lamba da kasar ta yi mata.
Idan muka waiwayi shekarar 2025, za mu ga cewa, ta kasance mai muhimmanci wajen gyare-gyaren tsarin kulawa da harkokin duniya. A yayin da ake fuskantar karin nuna fin karfi da rarabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, kasar Sin na hada hannu da kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa bisa shawarar GGI, don kafa tsarin kulawa da harkokin duniya mai adalci. A zahiri ne, shawarar na bude wani sabon babi game da makomar dan Adam.