Zamfara: ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,065 A Bukkuyum Tun 2015 – Shugaban Ƙaramar Hukuma
[ad_1]
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara, Abubakar Umar-Faru, ya ce ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 1,065 a yankin tun daga shekarar 2015.
Ya kuma bayyana cewa mazauna yankin sun biya kusan Naira biliyan 2.9 ga ’yan bindiga a matsayin kuɗin fansa da haraji.
- Ɗaliban Nijeriya Sun Nemi A Dakatar Da Dokor Haraji
- Mutane 4 Sun Rasu Bayan Motoci Sun Kutsa Cikin Gasar Al’adun Eggon A Nasarawa
Ya ce matsalar tsaro ta tilasta wa mutane da dama barin gidajensu tare da kawo cikas ga harkar noma da sauran harkokin tattalin arziƙi.
Umar-Faru ya ce dukkanin gundumomi 17 da ke ƙaramar hukumar sun fuskanci hare-hare da dama, inda al’umma ke biyan kuɗin fansa domin yin rayuwa.
Ya ƙara da cewa ’yan bindiga sun sace dubban shanu, awaki da kuma raƙuma.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce sama da mutane 200, ciki har da mata da yara, na hannun ’yan bindiga.
Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin soji mai tsauri, musamman a Gandun Dajin Gando, wanda ya zama mafakar masu laifi.
[ad_2]
Source link