Manufar Kawar Da Haraji Za Ta Bunkasa Cigaban Masana’antun Ghana

[ad_1]

Mahalarta wani taron tattaunawa game da raya tattalin arziki da ya gudana a kasar Ghana, sun jinjinawa manufar kasar Sin ta kawar da haraji baki daya, kan kayayyakin da ake shigarwa Sin daga kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da Sin. Suna masu bayyana manufar a matsayin muhimmin tafarki, na ingiza kudurorin raya tattalin arziki da masana’antun Ghana da ma na nahiyar Afirka baki daya.

Kungiyar raya kawancen Ghana da Sin ce ta shirya taron na yini daya a ranar Talata, bisa taken “Kawar da haraji baki daya na Sin da Afirka: Damammaki ga kasar Ghana”.

Yayin taron, babban mashawarci a fannin kasafin kudi a ma’aikatar kudi ta kasar Ghana Samuel Nii-Noi Ashong, ya bayyana manufar ta gwamnatin Sin a matsayin muhimmiya kuma mai cike da tarihi, yana mai kira ga kasar Ghana da ta yi amfani da hakan wajen sauya fannin masana’antunta, tare da lalubo kyawawan hanyoyin daidaita matsayar cinikayya tsakaninta da Sin a nan gaba.

Samuel Nii-Noi Ashong ya kara da cewa, manufar yafe harajin ta Sin, ba ta nufin su ma kasashen Afirka su janye haraji kan hajojin Sin dake shiga kasashensu. A cewar kwararren, wannan rangwame ya dace da sauran matakan tallafi da suka hada da gina kwarewa ta fuskar fasaha, ciki har da musayar ilimi, da tallafawa hada-hadar fitar da hajoji, da samar da ofisoshin cinikayya na musamman a Sin, da taimakawa wajen shigar da hajojin da aka sarrafawa a Ghana cikin babbar kasuwar Sin mai yawan al’umma biliyan 1.4. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *