ADC Ta Nemi Shugaban INEC Ya Yi Murabus

[ad_1]

Jam’iyyar ADC ta buƙace Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da dukkanin Kwamishinonin ƙasa su yi murabus ko a sauke su daga muƙamansu.

Jam’iyyar ta ce ba ta aminc da shugabancin INEC, tana mai cewa ba za su iya gudanar da sahihin zaɓe ba.

  • An Shiga Ruɗani Kan Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Gidan Yarin Kuje
  • 2027: Tinubu Na Son A Naɗa Shi Sarauta Ne, Ba Zaɓe Ba — Dino Melaye

Shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da tsoffin gwamnonin jihohi kamar Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi da Liyel Imoke.

Mark, ya kuma yi watsi da matakin da INEC ta ɗauka na janye amincewa da shugabancinsa da na Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola.

Ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da shirye-shiryenta.

Haka kuma, ya buƙaci ƙasashen duniya su lura da matakan da INEC ke ɗauka, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya zama barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *