Sojoji sun ceto wanda aka yi garkuwa da shi a iyakar Kano da Katsina




Sojoji Rundunar Haɗin Gwiwa (JTF) da ke Faruruwa a Ƙaramar Hukumar Shanono sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a kan iyakar jihar Kano da Katsina.

Rahotanni sun ce aikin ya gudana ne da safiyar Lahadi, 28 ga Disamba, 2025, bayan sojojin sun samu bayanan sirri kan motsin ’yan bindiga daga yankin Daurawa da Kira a Katsina zuwa Kano.

Kakakin Birget na 3, Manjo Babatunde Zubairu, ya bayyana cewa sojojin da ke aiki daga sansanin FOB Yankwada sun kai ɗauki domin dakile ’yan bindigar.

Ya ce sojojin sun yi musayar wuta da ’yan bindigar a Unguwan Dogo da Unguwan Tudu, amma ’yan bindigar suka gudu a tsorace zuwa yankin Matazu a Jihar Katsina.

An ce an ceto wanda aka yi garkuwa da shi mai suna Rabiu Alhaji Halilu mai shekara 38, wanda ya samu rauni a ƙafa sakamakon harbin bindiga.

Sojojin sun kuma ƙwato babura uku, wayoyi biyu, da kuma shanu da ba a san adadinsu ba da ake zargin an sace, amma aka bari yayin gudun ’yan bindigar.

Manjo Zubairu ya roƙi al’ummar yankin da su ci gaba da ba hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar bayar da bayanai na gaskiya da wuri, domin taimakawa wajen ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *