Majalisa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta jingine Sabuwa Dokar Haraji

[ad_1]



Majalisar Wakilai ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta jingine shirinta na fara aiwatar da sabuwar Dokar Haraji mai cike da ruɗani.

Ɓangaren Marasa Rinjaye a Majalisar sun buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar har sai kwamitin da Majalisar ta kafa domin bincikar zargin sauya dokokin, domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Sabuwar badaƙala ta kunno kai ne bisa zargin cewa an sauya dokokin harajin fa Majalisar ta amince da su, inda aka yi cushe kafin Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu a kai.

Lamarin da ya haifar da zargin akwai bambanci tsakanin dokokin da majalisa ta amince da shi da kuma wanda Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu a kai, aka wallafa a kundin gwamnati.

Ɓangaren Zartaswa ya nesanta kansa da zargin, inda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

A cewarsa, a iya sanin gwamnati, dokar guda ɗaya ce, idan da wata matsala, to daga ɓangaren Majalisa ne.

Tuni dai Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi domin gano gaskiyar lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *