Indomie Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Al’adu A Bikin Kamun Kifi Na Argungu Karo Na 61
[ad_1]
Kamfanin Indomie ya sake jaddada aniyarsa ta bunkasa al’adu a Nijeriya ta hanyar daukar nauyin tare da shiga Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Argungu karo na 61, daya daga cikin fitattun bukukuwan al’adun gargajiya a Arewacin Nijeriya.
An fara wannan biki tun shekarar 1934 domin wanzar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin mutanen Argungu da makwabtan su. Daga baya ya zama taron al’adu da ya samu karbuwa a duniya bayan da UNESCO ta sanya bikin cikin jerin bukukuwan al’adu na duniya a shekarar 2016. A bana ma an gudanar da bikin kamun kifin a ranakun Juma’a 13, ga Febarairu da Asabar 14 ga Febarairun 2026, dubban mutane daga ko’ina a fadin duniya sun halarci bikin a Jihar Kebbi, inda gasar kamun kifi a Kogin Matan Fada ta kayatar da masu kallo tare da kara nuna muhimmancin al’adun bikin.
- Sabuwar Gobara Ta Sake Tashi A Kano, Ta Ƙone Shaguna 50
- Babu Wani Abu A Alkur’ani Da Ya Zama Maimaici, Komai Yana Da Ma’anarsa
Bayan gasar kamun kifi da ta shahara, bikin ya kunshi nune-nunen al’adu iri-iri da suka hada da wake-waken gargajiya da raye-raye da baje kolin sana’o’in hannu da nunin kayayyakin noma da wasanni masu kayatarwa. Wadannan duk sun kara haskaka yalwar al’adu da bambance-bambancen al’adu a yankin.
Wani daga cikin mahalarta bikin ya ce, “Zakaran gasar da ya kama kifi kilo 59, wanda ya fi daukar hankali a taron na bana, ya samu kyautar motoci sababbi guda biyu da kuma kudade.”
Bukin yana kyautata tsarin zamantakewa da bunkasa tattalin arziki, Indomie ta kuduri aniyar ci gaba da tallafa wa wannan gagarumin taro da yake bunkasa ci gaba al’umma da kasa baki daya. Kamfanin ya kuma bayyana gamsuwarsa da kasancewa cikin bikin tare da bunkasa al’adu da karfafa kasuwanci da hadin kan jama’a.
Tallafin da kamfanin ya bayar ya nuna kudirinsa na karfafa hadin kai da bunkasa bikin da al’adu da kuma bunkasa ci gaban al’umma. Tsawon lokacin Indomie ta nishadantar da mahalarta irin wadannan bukukuwa da wasanni da shirye-shirye masu kayatarwa, tare da rabon kyaututtuka, lamarin da ya samar da kara dankon zumunci tsakanin kamfanin Indomie da masu amfani da kayan kamfanin.
[ad_2]
Source link