Sultan Ya Jagoranci NSCIA Wajen Neman Sake Fasalin Jadawalin Zaben 2027 Cikin Gaggawa
[ad_1]
Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ta yi kira mai karfi na a sake duba jadawalin zaben 2027 nan take, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana kwanan nan.
Babban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta nuna rashin amincewa kan tsara babban zabe ya ci karo da lokutan ibada na Musulunci.
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 2
- Ramadan: An Nemi Al’umma Su Tausaya Wa Junansu
A cikin wani sanarwar da Sakatare Janar na majalisar kolin, Farfesa Is-hak Oloyede, ya sanya hannu a kai, majalisar ta bayyana kin amincewarta da shawarar INEC na gudanar da zaBen shugaban kasa na 2027 a lokacin wata mai alfarma na Ramadan. Bugu da kari, majalisar ta nuna damuwa kan zaBen gwamnonin da aka tsara wadanda suka yi daidai da ranar bikin karamar sallah, babban bikin Musulunci da ke nuna kawo karshen watan Ramadan.
Saarwar ta bayyana rashin gamsuwar al’ummar Musulmi, inda majalisar kolin ta yi godiya ga yawan korafe-korafen da aka gabatar a ofishinta, bayan sanarwar hukumar zaBe cewa za a gudanar da zaBen shugaban kasa a lokacin watan Ramadan, sannan an shirya zaBen gwamnoni a ranar karamar sallah.
“Ko da yake wannan sanarwa da majalisar koli ta addinin Musulunci ga INEC ba sabon abu bane, wanda ya kamata INEC ta fara sanar da majalisar tun daga farko kafin ta fitar da jaddawalin zaBe 2027. Muna kallon abubuwan da ke faruwa sosai kuma muna tsammanin a yi bitarsu nan take. Wannan lamari yana nuna yadda majalisar ke ganin an yi watsi ko rashin la’akari da abubuwan da ke damun Musulmai da gangan,” in ji saarwar.
NSCIA ta kuma bayyana burinta na karin wayewar kai da lura da addinin Musulunci, wanda abubuwan da suka faru a kasa da kasashen wajen Nijeriya a tsakanin al’ummar Musulmi ba za su tabbata ba. Ta ambaci ayar Alkur’ani, “Inna ma’al ‘usri yusra” (Lallai a ciki kowane tsanani akwai sauki). Majalisar ta yi kira ga Musulmi su kasance masu tsayuwa ga imaninsu tare da jaddada cewa Musulman farko sun fuskanci irin wadannan manyan kalubale.
Sanarwar ta jaddada muhimmancin gaskiya dadagewa kan kyawawan halaye da karfin addu’a a matsayin hanyoyin da Allah zai inganta yanayi kuma ya ba da kwanciyar hankali.
[ad_2]
Source link