Amurka Ta Yi Iƙirarin Kama Shugaban Ƙasar Venezuela

[ad_1]

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasarsa ta kai hari kan ƙasar Venezuela, wanda a cewarsa hakan ya kai ga kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, tare da matarsa.

A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce an cafke Shugaba Maduro da matarsa ne a lokacin da aka kai harin, sannan aka fitar da su daga ƙasar.

  • Manyan Nasarorin Da Dr Matawalle Ya Samar A Sashen Tsaro
  • Da Sahalewar Nijeriya Bayan Samun Bayanan Sirri Amurka Ta Kai Hari — Tuggar

Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa an ƙaddamar da harin ne ta hanyar haɗin gwuiwa da jami’an tsaron ƙasarsa, yana mai nuni da cewa aikin ya kasance na musamman kuma cikin tsari.

Tun da daɗewa dai Amurka ke yin barazanar ɗaukar matakin soji a kan Venezuela, sakamakon tsamin dangantaka da ke tsakaninsu.

Idan har hakan ya tabbata, abu na gaba shi ne Amurka zata yi ruwa da tsaki wajen ɗora sabon shugaban da zai mata biyayya kamar yadda take burin yin hakan a ƙasar Iran.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *