Kwankwasiyya ba mallakin Kwankwaso kaɗai ba ce — Ɗangwani

[ad_1]



Ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Kano, kuma ɗaya daga cikin waɗanda kafa tafiyar Kwankwasiyya, Dakta Adamu Ɗangwani, ya musanta zargin cewa wasu tsoffin abokan siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun ci amanar tafiyar Kwankwasiyya.

Ɗangwani ya ce waɗanda ke yaɗa irin wannan magana ba su fahimci ma’anar cin amana ba.

Ya bayyana wa wata kafar labarai a Kano cewa tafiyar Kwankwasiyya ba daga Kwankwaso kaɗai ta samo asali ba, illa dai ƙungiya ce ta ’yan siyasa da masana da suka haɗu suka ƙirƙira tare da ba ta suna.

“Wanda ya ce mun ci amanar Kwankwasiyya bai san ma’anar cin amana ba. Mu ne muka ƙirƙiro ta, muka ba ta suna. Babu wanda ya ci amanar Kwankwaso, domin siyasa ra’ayi ce,” in ji shi.

Ya bayyana cewa su shida ne suka fito da sunan da kuma tsarin tafiyar Kwankwasiyya, ciki har da Salisu Buhari, Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon minista Borodo, Farfesa Umar Farouk, Rabiu Suleiman Bichi da shi kansa Ɗangwani.

Ɗangwani ya ƙara da cewa sauyin akala a siyasa abu ne na yau da kullum, ba kuma za a ɗauke shi a matsayin rashin aminci ba.

Ya jaddada cewa “Ko tsakanin uba da ɗa ana samun saɓani, amma daga baya suna haɗuwa suna girmama juna. Siyasa ba addini ba ce. ”

Ya ce rabuwarsa da Kwankwaso ta faru ne lokacin da ya yanke shawarar barin PDP ba tare da ya sanar da wasu daga cikin abokan tafiyarsa ba.

“Ni ba ni ne na bar Kwankwaso ba. Shi ne ya bar PDP ba tare da ya sanar da mu ba, ni kuma na ci gaba da harkokina a PDP,” in ji shi.

Ɗangwani ya kuma bayyana cewa rabuwarsu ba ta da alaƙa da fitowar Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takara.

Ya ce, “Lokacin da aka ba Abba tikitin takara, ni ne Daraktan Kamfen a PDP. Yanzu kuma gwamna yana zuwa wurinmu, za mu mara masa baya da kuma gwamnati.”

Ɗangwani ya nuna ƙwarin gwiwa cewa APC za ta yi nasara a Kano a nan gaba, inda ya yi kira ga jama’a da su mara wa jam’iyyar baya.

“Muna da fata cewa APC za ta lashe Kano, kuma muna kira ga jama’a da su goyi bayanmu,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *