Akwai Matsala Kasafin Ilimi Ya Tsaya Kashi 6 Zuwa 7 Tsawon Shekara Biyar —Masana
[ad_1]
Masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun nuna damuwarsu akan yadda ake ci gaba yiwa shi banagaren kwauron kudi lokacin da Nijeriya take kasafin kudi,inda suka ja kunne da maganar cewa ware ma bangaren ilimi kashi 6–7 na kasafin kudi haka abin yake a shekaru biyar da suka gabata, wanda kuma suke ganin hakan ba karamar illah zai yi wa sashen ba musamman ma irin dogon tsari na cimma muradan ci gaba.
Masu ruwa da tsaki sun tattauna da Jaridar LEADERSHIP wannan ya biyo bayan an gabatarwa majalisun kasa shi kasafin kudin na shekarar2026.
- Yadda Mutanen Gari Suka Ƙone Matashi Kan Ƙwace Waya A Kano
- ‘Yan Bindiga: ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Uku Gami Da Kwato Bindigar AK-47 A Gombe
Kasafin kudin na wannan shekarar mai naira fiye da Tiriliyan 58.18 bangaren ilimi, an ware ma shi kawai Naira Tiriliyan 3.52,wanda shi ne kusan kashi 6 ne.
Sai dai kuma, UNESCO ko kuma hukumar da ke karkashin majalisar dinkin duniya da ke kula lamarin ilimi, kimiyya,da al’adun gargajiya ta bada shawarar gwamnatoci dasu ware, a kalla ma bangaren ilimi, a kasafin kudin kasa a kalla kashi 15–20 na kasafin kudin kasa domin shi bangaren na ilimi, masu ruwa da tsaki sun ce abin bai kai yawan kudaden basu kai yawan yadda ake son amfani da su kudaden ba, wajen samarwa matasa dabarun da za su yi amfani da su wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
LEADERSHIP ta lura da cewar a shekarar 2022, wancan lokacin kasafin gwamnatin tarayya Naira Tiriliyan 17.13,inda aka ware ma sashen ilimi A 2023 kuwa da kasafin gwamnatin tarayya ya kai,Naira Tirliyan21.83, bangaren ilimi an ware ma shi Naira Tiriliyan 1.54 ko kuma kashi 7.
Sai shekarar 2024, kasafin kudingwamnatin tarayya ya kai Naira Tiriliyan 27.5, inda aka ware ma bangaren ilimi Naira Tiriliyan 2.18, shi ne ya kusa da kashi 7.9.
Ita kuwa shekarar 2025, da gaba daya kasafin kudin Naira Tiriliyan 54.99, bangaren ilimi ya samu Naira Tiriliyan 3.52, ko ace kashi 7.3.
Da yake sa albarkacin bakinsa, Dakta Sylbanus Ugoh, Shugaban kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa (ASUU) reshen Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja cewa ya yi yadda gwamnatin tarayya ta ke ware ma bangaren ilimi kashi 6 hakan shi ya sa ake fuskantar babbar matsala ce a shi bangaren na ilimi.
Ya ce sami irin kudaden da ake ware ma sashen ilimi abin sam yayi matukar yin kasa da kashi 15–26 wanda hukumar UNESCO ta ce hakan ne za’a rika ware ma ilimi, domin sai ta haka ne, za’a iya maganin matsalolin da ake fuskanta na abubuwan da za su taimaka yadda za’a samu cin gajiyar ilimi wajen bunkasa rayuwar al’umma domin hukumar kulawa da jami’oi ta kasa ta ce ya dace ayi,maganin matsalolin.
Kamar yadda ya ce, haka lamarin yake a kasafin kudin shekarar 2026 duk daya ne abin yake domin kuwa babu wani ci gaban da aka samu, saboda kuwa babu wata kasa da ilimin ta zai samu bunkasa muddin babu abubuwan da ya dace su taimakawa shi bangaren na ilimi.
Don haka ya yi kira da gwamnati ta yadda da cewa ilimi shi ne babban ginshiki na kwao ci gaban rayuwa ta kasa.
“Babu ta yadda za’a yi kashi na kasafin kudin dsa aka ware ma bangaren ilimi zai iya maganin duk wadansu bukatun da shi bangaren ilimi yake bukata.
Irin hakan lalle ya nuna gwamnati bata shirya kawo gyara ba kan lalacewar da abubuwn more rayuwa suka yi a Jami’oin Nijeriya, musamman ma idan aka ce idan shi abinda aka ware ma sashen na bangaren ilimin ne gaba daya.
“Lokacin da aka yi amfni da su kudaden ana iya fahimtar cewa babu wani abinda za su canza. An sa ran kasafin kudin shekarar 2026 kason na ilimi zai canza domin yin maganin matsalolin da ake fuskanta, ko da ma ace sun dan yi wani taimako da abin zai kasance sanadiyar kawo gyara ko ta wacce hanya zai iya samuwa. Amma da yake, da maganar Naira Tiriliyan , zai yi matukar wuya a samu wani ci gaba.
Ya ce “Za mu ci gaba da yin magana lokaci zuwa lokaci tare da fatan gwamnati za ta gane amfanin ilimi ga ‘yan Nijeriya. Babu wata kasa da zata samu wani ci gaba, ba tare da bunkasa tafarkin bangaren ilmin ta ba. Ilimi shi ne ke saita yadda ci gaba zai iya samuwa ga kowace kasa.”
Shi ma, a ma shi jawabin mai magana da yawun kungiyar daliban Nijeriya ta kasa, (NANS), Komrade Adeyemi Samson, ya yi maganar rashin jin dadi akan kashi 6 da ake ware ma bngaren ilimi a kasafin kudi na kasa wanda sam bai isa ba.
Duk da yake ya jinjinawa irin kokarin da gwamnati take yi wajen kawo ma sashen ilimi taimako, wato kamar hukumar bada bashi ko tallafin karatu (NELFund) ga kuma rage tafiya zuwa yaje- yajen aiki, ya yi kira da hukumomi, da suka hada da ma’akatar ilimi da fadar Shugaban kasa,su kara ma shi bangaren ilimi kaso lokacin kasafin kudi. Samson ya nuna da akwai bukatar taimakawa wajen samar da isassun abubuwan da za su taimaka wajen jin dadin karatu a makarantu, kudaden bincike da kuma irin wanda ake badawa lokacin kasafin kudi, domin a samu tafiya daidai da, yadda lamarin yake a wasu kasashen duniya, kamar shawarar da UNESCO ta bada na a kalla kashi 15 zuwa 20 wa bangaren ilimi.
Ya ce “Babu yadda za’a yi kungiya ta dalibai ta amince da lamarin kashi 6 na kudin da aka ware ma bangaren ilimi kamar yadda ya jaddada,”.
“Babban matakin da zamu dauka wand aba zai dauki lokaci mai tba shi ne su samu dama ta haduwa da hukumomin gwamnati wadanda suka kamata da, musamman ma ma’aikatar ilimi, shi Ministan da sauran masu ruwa da tsaki da za su iya sa, a samu kari na kason da ake ware ma shi sashen na ilimi.
“Hakanan ma mun yi shiri na saduwa da fadar Shugaban kasa, musamman ma shi Shugaban kasa, domin mu roke shi da ayi kari na kasafin da ake ware ma ilimi ya fi kashi 6.
Mun jinjinawa gwamnati kan irin matakan data dauka wajen taimakawar kamar kafa hukumar ba dalibai bashin karatu NELFund ke nan, sai kuma wasu abubuwan da aka lura da suke taimakawa ta wancan bangaren kamar rage tafiya yajin aiki na Jami’oi da wasu makarantu tun lokacin da wannan gwamnati ta fara wannan mulki.
“Duk da yake ganin yawan kudaden ko kason da aka ware yana da matukar amfani, sai dai wani abu daban shi ne yin amfani da kudaden da aka ware, a cikin kason shi ne abu mafi muhimmanci, irin hakan ba a damu da yin shi ba a shekarun da suka gabata na baya. Harkar ilimi tana bukatar sa ko zuba kudade wadanda zasu, maye gurbin duk wani abinda aka san za ayi ma shi bangaren ga kuma bangare na yin bincike da abubuwan da za su taimaka wajen jin dadin tafiyar da harkokin na karatu a makarantu, sun hada da dakunan gwaje- gwajen da suka amsa sunansu kamar yadda suke a kasashen da suka ci gaba.
“Za mu tabbatara da cewar hukumomin da suka kamata sun ji muryoyinmu, musamman ma Ministan ilimi, saboda shi ne zai yi iya yadda ya dace domin a samu kari a kason da ake ware ma shi bangaren na ilimi.”
Irin magana da shawarar da ya bada ke nan dangane yadda ake yi ma sashen na ilimi kwuron kudade kamar dai yadda Auwal Musa Rafsanjani, Babban jami’i na kungiya mai zaman kanta da ake kira da suna cibiyar al’umma mai sa idanu kan ana tafiyar da abubuwa ko ayyuka kamar yadda ya dace (CISLAC).Kasafin kudin Nijeriya na yadda aka ware ma sashen ilimi dan karamin kaso yin hakan bai ma kamata ba.
Kamar yadda bayanain na sa ya nuna kungiyar ta,CISLAC za ta ci gaba da yin maganganu wajen bada shawarwari na a kara tallafin da ake ware ma bangaren ilimi, a kasafin kudin da ake yi na shekara –shekara, kamar yadda hukumar UNESCO ta bada shawara na, a ware ma shi sashen ilimi, a kalla kashi 20 na kasafin kudin kasa ga bangaren ilimi, domin a tabbatar da cewar ana sanun ingantartar koyarwa, rage fatara da kuma samun daidaituwa, domin a samu dama ta bunkasa samar da kayan da za a yi amfani da su , wajen samar da ayyukanyi a masana’antu.
[ad_2]
Source link