Yadda Ake Hada Dilka Na Amare
[ad_1]
Kayan hadi:
Ruwan lemon tsami, Kwoi, Zuma, Ruwan madara cokali 3, Ruwan Sikari da kanwa kowace iri, Ruwan Alif kadan, Man Zaitun ba da yawa ba.
Wadannn su ne ruwan hadin Dilka.
Saura garin da ake hadawa:
- Lallan gargajiya, Garin ganyan magarya cokali 3, Garin yallon kurkur, da jan kurkur.(Tumeric ).
Sai Kuma Yadda ake hadawa:
Wadancan ruwayen da muka tanada da farko, da su za a hade su wuri daya a cakude su sosai a kuma tabbatar sun hade sosai. Sannan kuma wannan garikan suma azuba su cikin wannnan hadaddan ruwan adame su, su damu sosai, amma in an ga sun yi kauri da yawa to ana iya kara ruwan Alif da Sikari da kanwar nan don su dan yi daidai.
Shikenan sai a shafa wa Amarya aduk inda ake son a shafe. Bayan ‘yan mintuna kamar 30 sai a goge mata da manzaitun. Daga nan sai a yi wanka da dafaffen ganyan magarya a sa madarar turare mai kanshi irin wanda ake so. Wannan shi ne yadda ake hada Dilka na amare.
[ad_2]
Source link