An tarwatsa gungun ’yan fashi da makami a Gombe

[ad_1]



Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe ta tarwatsa wata ƙungiyar ‘yan fashi da makami da ke aiki a yankin Pindiga na Ƙaramar Hukumar Akko, tare da kwato makamai da harsasai.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 2:00 na ranar 29 ga Janairu, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewarsa, waɗanda aka kama sun haɗa da Babangida Gamji mai shekaru 25 daga ƙauyen Fobawure a Ƙaramar Hukumar Billiri da Dahiru Abdullahi mai shekaru 30 daga Wawa a Ƙaramar Hukumar Funakaye, da Ahmadu Garba mai shekaru 21 daga Ƙaramar Hukumar Song ta Jihar Adamawa, da kuma Umaru Bubba da ake kira Babuga mai shekaru 25 daga Dadin Kowa a Ƙaramar Hukumar Yemaltu-Deba.

Akwai kuma Isah Haruna mai shekaru 20 daga Dadin Kowa; da Unman Abdullahi mai shekaru 30 daga Kaltungo.

Sai dai ya ce wani daga cikin ‘yan ƙungiyar, Alhaji Sale Adamu, ya tsere wanda yanzu haka ake nema ruwa a jallo.

DSP Abdullahi ya ce ana zargin ƙungiyar da kai wa wani mutum hari a watan Disamba na shekarar 2025.

Ya ce “da misalin ƙarfe 2:30 na dare ne Babangida Gamji tare da wasu daga cikin abokan aikinsa suka kai masa farmaki a gidansa.

“Sun buga masa bindiga da adda tare da yunƙurin kwace babur ɗinsa. Ko da yake ya tsira daga harin, daga baya kuma sun riƙa kiransa ta waya suna masa barazana, tare da buƙatar kuɗin fansa naira dubu ɗari shida da hamsin (₦650,000), wanda daga bisani ya biya.

Bayan karɓar ƙorafin, DSP Abdullahi ya ce jami’an bincike suka fara zurfafa bincike, lamarin da ya kai ga kama babban wanda ake zargi da sauran abokan aikinsa guda biyar.

Ya ƙara da cewa sun ƙwato bindigar pump-action guda ɗaya, bindigar LAR da aka ƙera a gida guda ɗaya, harsasai 12 na 7.62mm, alburusai guda ɗaya, adda da kuma kuɗi naira ₦227,000 daga hannun ababen zargin.

Ya ce a halin yanzu waɗanda ake zargin na tsare a hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike, yayin da rundunar ke ƙara ƙaimi wajen kamo wanda ya tsere domin tabbatar da an hukunta duk masu hannu a lamarin.

A nasa jawabin, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar wa al’umma cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka samu a wurin ababen zargin


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *