An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara




An kama ’yan Najeriya uku a rukunin gidaje na Mwaliko da ke garin Mwea a ƙasar Kenya, bisa zargin su da damfara ta intanet.

Rahoton da wata kafar labarai a Kenya mai suna Tuko News ta fitar ya ce Hukumar Binciken Laifuka ta ƙasar (DCI) ce ta kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe.

A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, an kama su a gidansu bayan jama’a sun kai ƙorafi kan take-takensu musamman da daddare a cikin ginin.

DCI ta tabbatar da kama su, tana mai cewa an gudanar da “farmakin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da dama domin kama wata ƙungiyar masu damfara ta intanet” a yankin.

Rahoton ya ambato DCI tana cewa: “An kama ’yan Najeriya uku a wani farmakin haɗin gwiwa a Kirinyaga. Wannan farmaki da aka tsara sosai a rukunin gidaje na Mwaliko cikin garin Mwea ya tona asirin wata ƙungiyar masu damfara ta intanet da ’yan Najeriya uku ke gudanarwa.”

Waɗanda ake zargin sun ce suna gudanar da kasuwanci ta yanar gizo, amma rahoton ya nuna cewa suna zaune a Kenya ba tare da izini ba, kuma ba su da takardun aiki na doka.

Kamun nasu dai na cikin jerin kame-kamen da ake yi wa ’yan Najeriya a ƙasashen waje kan laifuka daban-daban, ciki har da damfara ta intanet, safarar miyagun ƙwayoyi, da safarar mutane.

Ko a watan Yunin 2023, sai da ’yan sandan a kasar ta Kenya suka kama ’yan Najeriya 19 a Nairobi, babban birnin kasar, bisa zargin damfara ta intanet da ke kai hari ga ’yan ƙasar.

A cewar DCI, mutanen da shekarunsu ke tsakanin 19 da 33, sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen fara damfarar, suna yaudarar ’yan Kenya da sunan za su tura musu kaya daga ƙasashen waje.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *