Sin Ta Yi Nasarar Harba Rukunin Taurarin Dan’adam Guda Biyu

[ad_1]

A yau Juma’a ne kasar Sin ta yi nasarar harba rukunin taurarin dan’adam guda biyu, masu aikin samar da hidimar intanet da wadanda aka tsara domin gudanar da gwaje-gwajen kimiyya.

An harba rukunin taurarin na farko ne da karfe hudu saura mintuna 12 agogon Beijing, daga cibiyar harba kumbuna ta Hainan, ta amfani da rokar Long March-8A. Rahotanni sun ce aikin shi ne irinsa karo na 20, na harba taurarin dan’adam marasa nisa daga doron duniya, domin samar da hidimomin intanet da kasar Sin ke gudanarwa.

A daya bangaren kuma, da karfe bakwai saura minti 27 na safiyar yau, aka harba rukunin taurarin dan’adam na biyu, daga cibiyar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan, ta amfani da rokar Long March-2D, inda karkashin wannan aiki aka yi nasarar harba taurarin dan’adam na Shiyan-30 mai lamba 03 da 04. Wadannan taurarin dan’adam za a yi amfani da su ne wajen gudanar da gwaje-gwaje na fasahohin nazarin doron kasa. Shi ne kuma karo na 632, da aka yi nasarar amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan’adama a kasar Sin. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *