’Yan bindiga sun kashe magidanci sun sace matarsa mai juna biyu a Kebbi




Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa magidanci, Sufiyanu Garba, sun yi awon gaba da matarsa mai juna biyu a yankin Badariya da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.

Wani ɗan uwan matar, Shehu Mohammed Yauri, ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hari gidan ƙanwarsa Zainab wadda take ɗauke da juna biyu a cikin daren Juma’a, inda suka harbe mai gidanta sannan suka yi awon gaba da ita.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni suka bazama domin gudanar da bincike tare da ɗana wa maharan tarko.

Ya ƙara da cewa, bayan faruwar lamarin, sun garzaya da Sufiyanu mai shekaru 35 zuwa asibitin Sir Yahaya Memorial, inda a nan ƙwararrun mahukunta kiwon lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.

Kakakin ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin mayar da lamarin hannun sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike mai zurfi.

Ya ce suna fatan binciken zai ba su nasarar ceto matar da kuma cafke duk masu hannu a lamarin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *