NFF Na Duba Yiwuwar Soke Wasan Sada Zumunci Da Kasar Iran

[ad_1]

Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta ce tana sa ido sosai kan rikicin da ke kara tabarbarewa tsakanin kasashen Iran, Amurka da Israila, yayin da rashin tabbas ke karuwa game da shirye-shiryen wasannin sada zumunta na kasa da kasa da tawagar kwallon kafa ta Nijeriya da takwararta ta kasar Iran, in ji wani rahoton da jaridar PUNCH Sports Edtra ta ruwaito.

Tun da farko an shirya Nijeriya za ta shiga gasar hadaka ta kasashe hudu da za a buga a Amman, inda Super Eagles za ta fafata da Iran a ranar 27 ga watan Maris kafin ta hadu da tawagar kwallon kafa ta Jordan mai masaukin baki a ranar 31 ga watan na Maris.

  • Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris
  • Duniya Ta Shaida Kokarin Sin Bisa Shirin Ci Gaban Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’Umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15

Hakazalika kuma ana sa ran tawagar kwallon kafa ta Costa Rica na cikin kasashen da za su buga karamar gasar, duk da haka an jefa shakku kan shirin bayan da Iran ta janye daga gasar a daidai lokacin da rikicin siyasa da na soja ke karuwa a Gabas ta Tsakiya, dan jaridar ESPN Colin Udoh ya ruwaito a karshen mako cewa masu shirya gasar suna binciken yiwuwar mayar da wasannin daga Gabas ta Tsakiya zuwa Turai saboda dalilai na tsaro.

Da yake magana da PUNCH Sports Edtra, daraktan sadarwa na NFF Ademola Olajire ya ce ana ci gaba da tattaunawa yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan lamarin, lokacin da aka tambaye su ko akwai wata kasa ta Turai da ake ganin za a iya mayar da gasar zuwa can, Olajire ya ce alhakin hakan yana kan masu shirya gasar.

Rikicin ya karu ne bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da wani hari na hadin gwiwa akan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya haifar da daukar fansa a duk fadin yankin, kasashe da dama tun daga lokacin sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka, wanda ya tilasta rufe sararin samaniya da kuma haifar da fargabar tsaro da suka fara shafar ayyukan wasanni.

Sakamakon janyewar Iran, shirin da aka yi na kasashen hudu tun da farko ba shi da tabbas, masu shirya gasar suna tunanin shirya wani wasa na sada zumunci tsakanin Nijeriya da Jordan a wani wuri mai tsaro a nahiyar Turai idan gasar ba za ta ci gaba kamar yadda aka tsara ba.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya Ibrahim Gusau ya nuna cewa hukumar har yanzu tana da lokaci domin tantance matakin da za a dauka, buga akalla wasa daya na sada zumunci a lokacin a watan Maris ya kasance babban abin da Super Eagles ke sa ido a kai, yayin da zakarun na gasar cin kofin Afirka sau uku ke ci gaba da kokarin ganin sun farfado ta tawagar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *