‘Yan Ta’adda Na Neman ‘Yan Matan Indiya Da Tabar Wiwi Da Hodar Iblis A Matsayin Kudin Fansa
[ad_1]
Kungiyar zamantakewa da siyasa ta kabilar Yarbawa, Afenifere, ta yi Allah-wadai da sabon yawaitar kutsen ‘yan ta’adda a yankin kudu maso yammacin Nigeria, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ceto yankin daga matsalar ‘yan bindiga.
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Asabar, Sakataren Yada Labarai na kungiyar na kasa, Jare Ajayi, ya bayyana damuwar al’ummar Yarbawa kan yadda ake samun asarar rayukan jama’a kusan kullum a jihohi da dama.
- Nijeriya Na Yunkurin Mayar Wa Da Manoman Tumatir Asarar Da Suka Yi Ta Naira Biliyan 1.3
Sun kuma yi nuni da yadda ake mummunar mu’amala da mutanen da aka sace, inda ake dukansu da wulakanta su ba tare da jin kai ba.
Ajayi ya kawo misalai na hare-hare da dama, ciki har da: hare-hare kan coci-coci, ofisoshin ‘yan sanda, gidajen jama’a da manyan hanyoyi a Ondo, kore al’ummomi daga garuruwansu a Jihar Kwara, kisan manoma da kai hari kan matafiya a kan hanyar Igbeti–Kisi a yankin Oke-Ogun na Jihar Oyo, da kuma munanan sace-sacen mutane a Jihar Ekiti, inda aka kashe wasu daga cikin wadanda aka sace sannan aka rike gawarwakinsu domin neman kudin fansa.
Kudin Fansa
Ya kara da cewa: “Babbar shaida ta rashin tausayi da mugunta na wadannan miyagu ita ce yadda suka nemi Naira miliyan 1.5, tabar wiwi (Indian hemp), hodar iblis (cocaine), wani maganin maye na roba da ake kira ICE, da kuma kwandunan giyar kwalba, domin a sako gawar wani mutum da ke hannunsu.”
Ya ci gaba da cewa masu garkuwa da mutanen har ma sun bukaci a kawo musu ‘yan mata budurwai a matsayin fansa domin su saki maza hudu da suka sace a baya.
A cewar Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Jare Ajayi: “Har zuwa kwanan nan, ana kallon gida a matsayin mafaka mai aminci. Abin takaici, hakan ba haka yake ba yanzu. Wasu ma’aurata an kai musu hari a gaban gidansu a Akure, a Jihar Ondo, inda aka harbi mijin yayin da yake kokarin hana sace matarsa.”
Ajayi ya kuma bayyana cewa Elder Igwe, mahaifin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi, an sace shi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci a ranar Lahadi, 1 ga Maris.
Haka kuma a Erinmope-Ekiti da ke Jihar Ekiti, an sace iyali guda mai mutum biyar da misalin karfe 7 na yamma, a lokacin da mutane suke sallar magariba a masallaci.
Ajayi ya kara lura cewa irin wadannan hare-hare na dogon lokaci ana samun su a jihohi da dama, ciki har da Jihohin Kwara, Filato, Binuwe, Borno, Kebbi, Nasarawa, Neja, Katsina, da Jihar Kaduna.
Ya kuma ce ’yan gudun hijira da suka dawo daga Kamaru su ma sun fada cikin irin wadannan hare-hare a Jihar Bauchi.
Da yake tuna wani lamari da ya faru a Jihar Edo, Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Jare Ajayi, ya bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka sace wani likita da dan’uwansa, inda suka kashe kanin amma suka saki likitan bayan an biya kudin fansa.
Ajayi ya ce: “Lokacin da ’yar daya daga cikin masu garkuwar ta kamu da rashin lafiya, likitan wanda ke bakin aiki a asibiti ya gane mutanen da suka aikata laifin, sannan ya sanar da ‘yansanda, lamarin da ya kai ga kama su.”
Ya kara da cewa: “Abin lura a nan shi ne cewa dan bindigar ya daraja rayuwar ‘yarsa har ya kai ta asibiti domin a kula da lafiyarta, amma a lokaci guda bai ga laifi ba wajen kashe rayukan wasu mutane.”
Ajayi ya jaddada cewa ta’addanci da sace mutane sun yawaita sosai, amma ya ce matsalar ba wadda ba za a iya shawo kanta ba ce, yana mai cewa:
“‘Yan bindiga ba aljanu ba ne kuma ba su da karfin da ba za a iya kayar da su ba.”
Daga nan ya yi kira ga a dauki mataki mai karfi domin katse hanyoyin da ‘yan bindiga ke samun kudi, wadanda suka hada da:
Wasu attajirai marasa gaskiya, kungiyoyin gida da na kasa da kasa, wasu jami’an gwamnati, al’ummomin da ke biyan kudin kariya ko kudin girbi, kudin fansa daga wadanda aka sace, da kuma sata kai tsaye.
Masu Hakar Ma’adanan Kasar Waje
Ya kuma yi kira a gudanar da bincike kan ’yan waje da ke da hannu a cikin harkokin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, wadanda ka iya zama suna jawo korar al’ummomi daga garuruwansu.
“Bayanan da aka samu daga ’yan bindiga da aka kama kuma aka gurfanar da su sun nuna cewa suna da masu daukar nauyi. Saboda haka, yana da muhimmanci a bi diddigin masu daukar nauyin da masu shiga tsakani, katse hanyoyin samun kudade da makamai, kai farmaki a dazuzzukan da suke boye, magance cin hanci da barnar da ke cikin hukumomin tsaro, karfafa ma’aikata, da tabbatar da kafa ‘yan sanda na jiha nan da nan,” in ji Ajayi.
Afenifere ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda jajircewarsa wajen ci gaba da kafa ‘yan sanda na jiha, tana mai jaddada kira da ya yi ga Majalisar Kasa da ta hanzarta gyara kundin tsarin mulki don tabbatar da fara aiki nan take.
Haka kuma an yabi sabon Sufeto Janar din ‘yansanda, Tunji Disu saboda kafa kwamitin da zai tsara hanyoyin da za a yi amfani da su wajen tura ‘yan sanda na jiha.
Kungiyar ta sake jaddada kiranta ga gwamnonin kudu maso yamma da su aiwatar da matakai na kai farmaki a boyayyun wuraren ‘yan bindiga, kula da yankunan da suka fi fuskantar barazana, da hadin kai sosai da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da kafa ‘yan sanda na jiha cikin gaggawa a jihohinsu.
[ad_2]
Source link