Shugaban Seychelles Ya Jinjina Wa Kasar Sin Game Da Nasarorin Da Ta Cimma
[ad_1]
Kwanan baya, shugaban kasar Seychelles Patrick Herminie ya zanta da dan jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a fadar shugaban kasar Seychelles, inda ya jinjina wa kasar Sin game da nasarorin da ta cimma.
A yayin zantawarsu, shugaba Herminie ya mika sakon gaisuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping. Haka kuma, ya ce, shekarar 2026 ita ce ta cika shekaru 50 kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Seychelles, cikin wadannan shekaru 50, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin ba da taimako ga kasarsa wajen gina ababen more rayuwa, da kara karfin kasa, da kuma ba da horaswa ga ma’aikata da dai sauransu. Kuma, yana fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu domin cimma moriyar juna.
Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, kasar Sin tana kan gaba a fannoni da dama, musamman ma a fannin bunkasar kimiyya da fasaha, da fasahohin sadarwa da kuma fasahar AI da dai sauransu. Kasar Seychelles tana fatan raya hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin kan wadannan fannoni, domin koyon fasahohi da dabarun kasar Sin, ta yadda za su ba da gudummawar raya kasar Seychelles.
Haka zalika, kasar Seychelles ita ce kasa mafi kusa da kasar Sin a duk fadin nahiyar Afirka, shi ya sa, shugaba Herminie ya ce, ta kasar Seychelles, kasar Sin za ta kara mu’amalar al’adu da harkokin cinikayya a tsakaninta da kasashen Afirka. Domin a ganinsa, wannan wurin da kasar Seychelles take, ya sa, kasar ta kasance muhimmin bangare da zai ba da gudummawar raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” a nahiyar Afirka. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link