Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu




Shugaba Bola Tinubu, ya ce kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga hanyoyin da ba na man fetur ba sun isa wajen daƙile tasirin manufofin tattalin arziƙin shugaban Amurka, Donald Trump.

Trump, ya sanya sabbin dokoki, ciki har da haraji masu tsauri, wanda suka jawo suka daga sassa daban-daban na duniya.

Yayin da yake karɓar tawagar ‘The Buhari Organisation’ ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Almakura, a fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce Najeriya ta riga ta cimma burin samun kuɗaɗenta na shekarar 2024 tun daga watan Agusta.

“Mun riga mun cimma burin samun kuɗin shiga na wannan shekara tun a watan Agusta.

“Kuɗaɗen da ba na man fetur ba ne, ba ma jin tsoron abin da Trump yake yi a can,” in ji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta daidaita tattalin arzikin ƙasa tare da rage dogaro da man fetur, don haka matsin lamba daga waje ba zai hana ci gaba da samum kuɗaɗen ƙasar ba.

Trump ya sha kiran ƙungiyar OPEC da ta ƙara fitar da adadin mai domin rage farashinsa a duniya.

A watan Yuli, OPEC da abokan haɗin gwiwarta sun amince da ƙara samar da ganga dubu 548 a kowace rana daga watan Agusta.

A watan Afrilu kuma, Trump ya sanya wa ƙasadhe haraji, ciki har da kaso 14 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya.

Bayan haka ya sanya hannu kan dokar dakatar da rangwamen haraji ga ƙasashe a ƙarƙashin dokar gaggawa ta tattalin arziƙin Amurka.

A shekarar 2023, Najeriya ta fitar da kaya zuwa Amurka da suka kai dala biliyan 6.29.

Daga Cikinsu akwai man fetur mai na dala biliyan 4.73, gas dala miliyan 920, da takin zamani dala miliyan 167.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *