Me Ya Sa Ake Yawan Nuna Wa Vinicius Wariyar Launin Fata?

[ad_1]

Kawo yanzu dai ɗan wasa Vinicius ya fuskanci kalaman nuna wariya sau 20 a zamansa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid tun bayan komawarsa ƙungiyar a shekara ta 2018. Wannan karon ɗanwasan ya zargi ɗan asalin ƙasar Argentina Gianluca Prestiani da yi masa kalaman nuna wariyar launin fata.

Sai dai Prestianni ya musanta zargin, sannan ɓinicious ya samu goyon bayan fitattun Ƴan ƙwallo, ciki har da Kylian Mbappe, wanda ya ce ya ji kalmar nuna wariya sau biyar.

  • Da Ɗumi-ɗumi: Mbappe Ba Zai Buga Wasan Real Madrid Da Benefica Ba
  • Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Amma kuma bayan tashi daga wasan, kocin Benfica Jose Mourinho ya zargi ɗanwasan da janyo wa kansa, musamman kan irin murnar da ya yi bayan zura ƙwallon. Mourinho ya ce ba zai yiwu ƙungiyar Benfica ta zama ƙungiyar nuna wariyar launin fata ba, domin a cewarsa, fitaccen ɗanwasan ƙungiyar a tarihinta, Euseubio ma baƙar fata ne.

A wani ɓangaren kuma a duk lokacin da ɓinicious ya fuskanci masu kallo, ana masa kallon girman kai da nuna isa. Amma kuma ana fassara hakan a matsayin nuna rashin amincewa da nuna wariya da yake fuskanta. Frantz Fanon ya bayyana a wani littafi da ya rubuta a shekarar 1952 mai suna, Black Skin, White Masks cewa: “dole baƙaƙen mutane su yi ƙoƙari ninki biyu na ƙoƙarin fararen mutane domin su samu karɓuwa.”

Wataƙila wannan ne Vinicious ke kallo ya sa yake yawan fushi da ƙara ƙaimi domin nuna ƙwanji, wanda wasu ke ganin yana wuce ƙima. ɓini Jnr dai ya zama sha gwagwarmaya sha fama a Sifaniya, inda har a kotu ya bayyana domin bayar da bahasi, sannan an sha dakatar da masu kallo da dama saboda shi.

A watan Oktoban 2021 a wasan Classico a filin wasa na Camp Nou, wani ɗan kallo ya yi masa kalaman wariya bayan an cire shi a wasan. Sai dai Ƴansanda ba su samu nasarar gano mutumin ba. Sannan a watan Maris na 2022, magoya bayan ƙungiyar Mallorca ne suka masa ihun biri, sannan suka ce ya “ɗauki ayaba.”

Hukumomin ƙwallo sun nuna ɓacin rai, amma ba a ɗauki wani mataki ba. A wani shirin wasanni mai suna El Chiringuito a Sifaniya, shugaban ƙungiyar wakilan Ƴan wasa na Sifaniya Pedro Braɓo, ya yi kira ga ɓini da ya “daina yin abu kamar biri,” sannan ya riƙa girmama abokan karawarsa. Daga baya ya janye kalamansa, sannan ya nemi afuwa tare da cewa kwatance kawai ya yi, amma ba a ɗauki wani mataki ba.

A watan Satumban 2022, magoya bayan Atletico Madrid sun masa waƙar nuna wariya, amma ba a ɗauki wani mataki ba. A watan Janairun 2023, an ga hoton wata ‘yar tsana an saƙale ta sanye da rigar ɓini. An kama mutunen da suka aikata laifin, sannan aka tura su gidan yari, kafin daga baya aka mayar da hukuncin ya zama biyan kuɗin tara.

Lokacin da abin da ya ɗauki sabon salo shi ne a wasan ɓalencia a watan Mayun 2023, inda ɓini ya fuskanci sashen masu kallo da suke masa kalaman ɓatanci. Daga baya kuma aka nuna masa jan kati bayan ya yi musayar yawu da mai tsaron ragar ɓalencia Giorgi Mamardashɓili da ɗanwasan ƙungiyar Hugo Duro.

A watan Yunin 2024, an kulle mutum huɗu bisa samunsu da laifin nuna masa wariya, inda aka yanke musu hukuncin ɗaurin wata takwas da kuma hana su kallon wasa na shekara biyu. Wasu lokutan ma ana nuna masa kalaman wariya ko da ba ya cikin filin wasan, domin a filin wasa na Mestalla, ana wasa ne tsakanin Atletico Madrid da Inter, amma Real Madrid ta kai ƙorafin an ci zarafinsa.

Sannan a wani wasan bayan kwana biyar, a filin wasan Osasuna an riƙa yi masa waƙar, “ɓinicius sai ya mutu.” A ranar 29 ga Satumban 2024, an kama mutum huɗu da zargin nuna kalaman wariya a kafofin sadarwa ta hanyar ɓoye suna domin cin zarafin ɗan wasan a wasan Madrid da Atletico.

Na baya-bayan nan shi ne watan Fabrairu, a wasan kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Rey tsakanin Real Madrid da Real Sociedad, alƙalin wasa Jose Maria Martinez ya tsayar da wasa saboda nuna wariya. A lokacin an nuna wa wani ɗanwasan daban ne wariya, amma da na’urar ɗaukar hoto ta zagaya, sai aka ga hango wani yana kwatanta ɓini da biri.

A watan jiya, a wasan farko da Alɓaro Arbeloa ya jagoranci Real Madrid, wasu magoya bayan sun nuna wa ɓini Jnr wariya, inda hukumar La Liga ta nuna masa goyon baya. Sai kuma wannan wanda ya faru a birnin Lisbon na ƙasar Portugal, a wasan cike gurbi na gasar cin kofin zakarun turai tsakanin Real Madrid da Benfica.

A game da abin da ya sa yake yawan mayar da martani kan masu nuna masa wariyar, ya bayar da amsa a watan Yunin 2024 bayan wasan Real Madrid da ɓalencia, inda ya ce, mutane suna cewa ya daina kula su, wasu na cewa babu abin da zai iya amma kamar yadda yake yawan faɗa, yana alfahari da cewa waɗanda aka fara yanke wa hukunci a Sifaniya saboda nuna wariya, shi ne ya yi sanadi. Wannan nasara ce ta baƙaƙen fata baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *