Ramadan: Kamfanin Indomie Ya Shirya Shan Ruwa A Gidajen Kwastomominsa A Kaduna
[ad_1]
Kamfanin taliyar Indomie ya shirya wani taron shan ruwa na musamman a Jihar Kaduna domin karrama mutanen da suka yi nasara a gasar tambayoyin Ramadan da aka gudanar ta gidajen rediyo a jihar, kamar yadda ake yi a jihohin Kano da Sakkwato, tare da ƙara ƙarfafa alaƙa da al’umma a wannan wata mai alfarma.
Shirin na daga cikin shirye-shiryen da kamfanin ya tsara domin samar da farin ciki a lokacin buɗa-baki tare da kwastomominsa da suka halarci gasar amsa tambayoyin da aka gabatar a gidajen rediyo a lokacin watan Ramadan.
- Indomie Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Al’adu A Bikin Kamun Kifi Na Argungu Karo Na 61
- NAFDAC Ta Haramta Shigo Da Indomie Saboda Zargin Sanya Ciwon Daji
Nura Yusuf Muhammad da Maryam Husaini ne suka zama zakarun gasar tambayoyin a Jihar Kaduna, bayan sun nuna ƙwarewa wajen amsa tambayoyin da aka gabatar a shirin.
Domin murnar wannan nasara tasu, Indomie ta shirya wani taron shan ruwa na musamman a Unguwar Millennium City da ke jihar, inda waɗanda suka yi nasara tare da iyalansu da sauran al’ummar yankin suka taru domin buɗa-baki tare da Indomie.
Taron ya samar da yanayi na farin ciki da annashuwa ga mahalarta, inda aka raba abinci da kuma kyaututtuka a lokacin buɗa-baki.
A yayin taron, waɗanda suka yi nasara sun bayyana farin cikinsu tare da nuna godiya ga kamfanin Indomie bisa wannan karramawa da aka yi musu. Sun ce shirin ya ƙara sanya musu farin ciki a watan Ramadan tare da ba su damar yin buɗa-baki tare da iyalansu da maƙwabta cikin annashuwa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasara ya bayyana cewa wannan kyakkyawan shiri ya sa watan Ramadan ya zama abin tunawa a gare su, tare da ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yaba da wannan shiri, inda suka ce irin wannan ɗawainiya ta kamfanoni masu zaman kansu irin Indomie na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kai da taimakon juna a tsakanin al’umma a wannan lokaci na Ramadan.
Da yake jawabi a wajen taron, wakilin kamfanin Indomie, Gabriel Ajeh, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin kamfanin na kusantar al’umma tare da karrama waɗanda suka halarci gasar tambayoyin Ramadan.
Ya ƙara da cewa karrama waɗanda suka yi nasara a irin wannan taro na shan ruwa na taimakawa wajen sanya shirin ya zama abin tunawa, tare da ƙarfafa alaƙa tsakanin kamfanin da kwastomominsa.
Har ila yau, kamfanin Indomie ya faɗaɗa damar shiga gasar ta hanyar shafukansa na sada-zumunta na yanar gizo mai suna Indomie Arewa, inda ake wallafa tambayoyi a kowace rana domin bai wa waɗanda ba su samu damar sauraron shirin rediyo ba damar shiga gasar.
Mutanen da suka amsa tambayoyin daidai a waɗannan shafuka na sada-zumunta suna samun kyautar kwalin taliyar Indomie domin taimaka wa iyalai a wannan lokaci na watan Ramadan.
Kamfanin ya bayyana cewa wannan shiri na nuna ƙudurinsa na tallafa wa al’umma da kuma samar da farin ciki a tsakanin jama’a a watan Ramadan mai alfarma.
[ad_2]
Source link