Hobbasar Gwamna Abba Kan Titunan Birnin Kano

[ad_1]

Kamar dai yadda kowa ya sani ne, kowace gwamnati na kammala wa’adin lokacinta, ba tare da ta gama dukkan ayyukan da ke gabanta ba. Sau da dama, za ka ga idan gwamnati ta tafi, wata ta zo, za ka ga an samu wasu ayyukan da gwamnatin da ta gabata ba ta iya yi ba, ko ba ta samu damar yin su ba.

Haka lamarin yake, kafin shigowar gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano, akwai wasu tituna masu muhimmanci a cikin kwaryar birni, wadanda gwamnatin baya ba ta samu yin su ba. Ba wai babu titunan ba ne a wuraren, a’a sai dai kawai sun lalace yadda suke jawo cunkushewar hanyoyin sufuri tare da jawo hadura a wasu lokutan.

  • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
  • Majalisar NPC Ta Gudanar Da Zaman Rufe Taronta Na Shekara-shekara Na Bana

Domin kauce wa matsalolin da ire-iren wadannan lalatattun tituna ke haifarwa, sai gwamna ya shigo da wani tsari na kula da titunan cikin birni da ya ba shi suna; “Urban Renewal Project.”

Ta karkashin wannan shiri ne aka samu aka duba titunan da suka ji jiki, suke kuma kawo tare da kara cunkoson ababen hawa, babu gaira babu dalili. Amman fa hanyar da aka fito da ita wajen tantance ire-iren titunan da za a taba, ta taimaka matuka gaya wajen lalubo wuraren da suka dade a dankwafe, ba tare da kula ba yadda ya kamata.

Wannan fa ba kuma a maganar wasu katafaren gadoji da gwamnatin ke yi a halin da ake ciki ba. Akwai katafariyar gadar Tal’udu da kuma daya katafariyar gadar ta Kofar Dan Agundi. Dukkan wadannan gadoji, an yi nisa sosai a aikinsu. Sannan kuma, irin gadojin nan ne na ‘da gani babu tambaya’. A nan, ina maganar yadda ayyukan ke da karko da kuma kayatarwa.

Daga lokacin da aka kammala wadannan gadoji, za kuma a ga da wace fuska ce kuma abokan adawar siyasa, masu cewa gwamna Abba bai taba kammala wani ko wasu katafaren ayyuka ba, tun bayan shigowarsa, za su kalli mutane? A nan, ba fa ana maganar wasu ayyukan da aka rigaya aka kammala ba.

Kasancewar shi birnin Kano ya shahara wajen samun yawan zirga-zirga na ababen hawa da ma wadanda ke tafiya kafafuwansu, ya sa gyare-gyaren titunan da ake yi suka yi tasirin gaske, wajen kara saukaka wa al’umma wahalar sufuri a cikin birnin na Kano.

Kasancewar Kano garin kasuwanci ne, hakan ta sa aka kara samun sauki da walwala wajen zirga-zirgar harkokin kasuwanci a cikin kwaryar birnin na Kano. Musamman ma da yake wasu daga cikin titunan da aka kammala ko aka kusa kammala gyaransu, suna da alaka ta kut-da-kut na kusanci da wasu kasuwannin namu.

A dai karkashin wancan shiri na ‘Urban Renewal Project’, gwamnatin ta mai girma Abba, ta kammala gyaran titunan, Lodgeroad da Murtala Muhammad Way da titin Airport da Club road da titin Yahaya Gusau da Titin Sharada da kuma sauran makamantansu. Ba wai gyara titunan ba kawai, an kawata su, kuma an yi musu aiki mai karko da kyawun gani.

Baya ga wadanda aka kammala yin su, akwai kuma wadanda a halin yanzu ana kan yin nasu gyaran. Wasu an kusa kammala su. Daga cikin wadanda ake kan aikin nasu, akwai titin Audu Bako da Lamido Crescent da Sulaiman Crescent da titin da ya kewaye kasuwar Farm Centre da Katsina road da titin Sabo Bakinzuwo da kuma titin Amadu Sambo, wanda ya taso daga titin Gandun Albasa zuwa titin Sharada.

Babban abin ban sha’awar ma shi ne, yadda jama’ar da ke amfana da wadannan hanyoyi ke nuna farincikinsu ga wadannan gyare-gyare da ake yi, tare da kara yaba wa zurfin tunanin gwamnan, musamman wajen gano cewa; ya kamata a sauwaka wa mutane ta bangaren gyara tituna, domin samun sufuri mai inganci a birnin na Kano.

Da yawa daga cikin wasu da na dan yi wani kwarya-kwaryar bincike a kai sun tabbatar da cewa, ba wai samar da kyawawan hanyoyin kawai ba, sun ma tabbatar da cewa; hatta ababen hawansu, sun kara samun lafiya. Saboda an fara ceto ababen hawan nasu daga kwazazzaban da suka yi wa titunan kaca-kaca kafin wannan lokaci.

Misalin titunan Lodge road da na Sabo Bakinzuwo, wadanda daya yake jikin gidan Gwamnatin Jihar Kano, da kuma dayan da ke tsallaken gidan gwamnatin, ba karamar dabara aka yi ba, wajen yi musu gagarumin aikin da ake kan yi musu. Misali, shi Lodge road, an kammala gyara shi har ma an sa masa fitilu da wasu furanni masu kayatarwa. Sannan ga magudanan ruwa na zamani da aka yi musu.

Yanzu ba abu ne mai wahala ba, idan aka ce wanda ya dan yi ‘yan watanni bai shiga Kano ba, idan ya je yanzu daidai yake da ya bata bata, saboda yadda ake ta kawata wurare da hanyoyi babu kakkautawa. Wannan shirin na kyautata titunan cikin birni, ya yi daidai da yadda gwamnan ke yi, wajen kula da wasu bangarori na gwamnatinsa.

Wani babban abin kawatarwa kuma shi ne, yadda aka kara buda titunan, domin su kara fadi a samu isassun hanyoyin sufuri, ba tare da samun wani cikas a nan gaba ba.

Haka zalika, wani abin ban sha’awa ma ga wannan hobbasa da gwamnan ke yi shi ne, tun bayan hayewarsa kan karaga mulkin, ya sha alwashin inganta bangaren sufuri a jihar, wanda hakan ya hada da kara inganta hanyoyin sufurin da ya hada da titunan da kuma sauran ababen sufurin, wato ababen hawa na al’umma.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *