Sojoji sun halaka shahararren Kwamandan ISWAP a Borno

[ad_1]



Sojojin rundunar haɗin gwiwa ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe Sa’ad, wani babban kwamandan ISWAP wanda ya addabi al’ummomin tafkin Chadi da yawaitar hare-haren ta’addaci a yankin.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an kashe Sa’ad a ranar Talata ne a lokacin wani mummunan artabu da aka yi a Doron Baga, ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Majiyar tsaro na cewa, wannan Kwamandan na ISWAP ya shahara wajen kitsa munanan hare-hare, sace-sacen mutane da kuma sa haraji ba bisa ƙa’ida ba ga masunta na yankin.

Ya mallaki manyan sassan hanyar ruwa, wanda hakan ya tilasta wa mazauna yankin biyan haraji don samun izinin kamun kifi.

A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’addan sun kai hari a Doron Baga da misalin ƙarfe 1:00 na safe, inda suka isa da yawa a kan babura da kwale-kwale.

Sojoji, ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar A.E. Ozemhoya, sun mayar da martani da ƙarfin wuta, inda suka daƙile harin tare da haifarwa ‘yan ta’addan asara mai yawa.

’Yan ta’addan sun gudu, da yawa suna ɗauke da gawarwakin su ‘yan uwan su ne da aka kashe a wannan gumurzu yayin da, da yawa daga cikin su suka tsere da munanan raunuka.

A ranar Laraba, majiyoyi sun tabbatar da cewa Sa’ad yana cikin waɗanda aka kashe yayin da mazauna yankin suka ce an yi jana’izarsa a wannan rana.

An bayyana Sa’ad a matsayin babban mutum a hare-haren da aka kai wa manoma, masunta da ‘yan kasuwa, kuma ya daɗe yana zama abin tsoro a yankin.

Wani memba na rundunar haɗin gwiwa ta farar hula ya jaddada cewar da hannun Sa’ad a hare-hare da dama a wannan yankin na tafkin Chadi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *