Jakadan Sin Ya Gana Da Shugaban Kasar Nijer

[ad_1]

Jakadan Sin dake kasar Nijer Lv Guijun ya gana da shugaban kasar Nijer Abdourahamane Tiani.

Yayin ganawar, shugaba Tiani ya bayyana cewa, shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da shawarwari 4 na tafiyar da harkokin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar sun samar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba a duniya, da kafa tsarin tafiyar da harkokin duniya mai adalci. Ya ce kasar Nijer tana son hada hannu da kasar Sin wajen kara mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni bisa tushen taron tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da tsarin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, ta yadda za a ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da amfanawa jama’arsu baki daya.

Hakazalika, shugaba Tiani ya jaddada cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin kasar Nijer tana goyon bayan hakan, da kin amincewa da wasu kasashe su yi amfani da batun kare hakkin dan Adam wajen tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran kasashe. Ya kara da cewa, kasar Nijer za ta ci gaba da nuna goyon baya ga matsayin Sin kan batutuwan yankin Taiwan, da kare hakkin dan Adam da sauran batutuwan dake shafar moriyar kasar Sin. Kana Nijer tana son ci gaba da hadin gwiwa da kasar Sin kan harkokin kasa da kasa don kare moriyar kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *